Zababun 'yan majalisan APC 16 a Sokoto sun ki zuwa karbar takardan shaidan cin zabe

Zababun 'yan majalisan APC 16 a Sokoto sun ki zuwa karbar takardan shaidan cin zabe

Zababun 'yan majalisar dokokin jihar Sokoto 16 na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) sun ki hallartar taron karbar takardan shaidan lashe zabe da INEC ta shirya a jihar.

A wurin taron, Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta mika takardun shaidan lashe zaben ga zababen gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, zababen mataimakinsa, Mannir Dan'iya da wasu zababun 'yan majalisar dokokin jihar.

Sai dai zababun 'yan majalisu na jam'iyyar APC ba su hallarci taron ba. APC ta lashe kujeru 16 daga cikin 30 yayin da ita kuma jam'iyyar PDP ta lashe sauran kujeru 14.

Zababun 'yan majalisan APC 16 a Sokoto sun ki zuwa karbar takardan shaidan cin zabe
Zababun 'yan majalisan APC 16 a Sokoto sun ki zuwa karbar takardan shaidan cin zabe
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Takarar kujerar DSP: Sanatoci 56 suna goyon baya na - Kalu

A halin yanzu ba a san dalilin da yasa 'yan jam'iyyar na APC na ba su hallarci taron ba da aka gudanar a Cibiyar karatun Al-Kurani na Sultan Muhammadu Maccido da ke Sokoto.

Sakataren yada labarai na APC a jihar, Sambo Bello Danladi ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa akwai yiwuwar hare-haren da ake kaiwa magoya bayan jam'iyyar APC a jihar ne dalilin da yasa suka ki zuwa.

"Magoya bayan jam'iyyar PDP suna kaiwa magoya bayan jam'iyyar mu hari a gidajensu da wuraren taro. Watakila wannan shine dalilin da yasa suka yanke shawarar kin zuwa taron. Za su karbi takardun shaidan na su daga baya," inji shi.

A bangarensa, Gwamna Aminu Tambuwal ya yi kira ga 'yan jam'iyyar APC su hada hannu da shi wurin kawo cigaba a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel