Namdas na neman kujerar Kakakin Majalisa Wakilai

Namdas na neman kujerar Kakakin Majalisa Wakilai

- A yanzu dai kowa na ta faman tallata hajarsa a majalisar wakilai, da ta dattawa, domin samun shugabancin majalisun guda biyu

- Hakan ne ma ya sanya Namdas fitowa neman takarar kakakin majalisar wakilai, domin cike gurbin tsohon kakakin majalisar Yakubu Dogara, wanda ya koma jam'iyyar PDP

Mai magana da yawun majalisar wakilai ta tarayya, Abdulrazak Namdas (APC Adamawa), ya bayyana burinsa na fitowa neman takarar kujerar Kakakin Majalisar Wakilai.

Namdas wanda ya bayyana hakan jiya Talata, 26 ga watan Maris, a Abuja, ya ce ya san ba abu bane mai sauki, amma duk da haka ya fito neman takarar kujerar. "Ina da kwarewa a fannin majalisa, saboda na rike mukami na mai magana da yawun majalisar nan, na tsawon shekaru hudu, saboda haka ina da kwarewar da zan rike mukamin Kakakin majalisar nan," inji Namdas.

Namdas na neman kujerar Kakakin Majalisa
Namdas na neman kujerar Kakakin Majalisa
Asali: Original

Namdas ya ta ya shugaban kasa Muhammadu Buhari murnar cin zabe a karo na biyu, sannan ya ta ya dukkanin 'yan majalisar wakilai akan nasarar da suka samu.

A lokacin da ya ke jawabin nasa, Namdas ya yi alkawarin cewa ba zai taba bari ayi abubuwan da basu da ce ba muddin yana kan kujerar Kakakin majalisar. Sannan ya roki 'yan majalisar wakilan da su zabe shi domin kawo cigaba a kasar nan.

KU KARANTA: Kahutu Rarara: Dalilin da ya sa nayi wakar 'Ta leko ta labe'

A bayanin da ya yi Abdulrahman Shaibu (APC Adamawa), ya shawarci jam'iyyar APC da ka da ta yanke hukuncin da zai zo bai yiwa kowa dadi ba. Ya bukaci jam'iyyar da ta bari 'yan majalisar wakilaisu zabi wanda zai shugabance su.

"Ka da mu bari abinda ya faru a shekarar 2015 ya sa ke maimaita kan sa, a bar 'yan majalisa su zabi shugaban su, saboda sun san wanda ya kamace su," inji Shaibu.

Wannan shine karo na biyu da Namdas zai dawo majalisar wakilai, bayan ya samu nasarar lashe zabe a karo na biyu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel