Kahutu Rarara: Dalilin da ya sa nayi wakar 'Ta leko ta labe'

Kahutu Rarara: Dalilin da ya sa nayi wakar 'Ta leko ta labe'

Shahararren mawakin siyasar nan na arewacin Najeriya Dauda Kahutu Rarara, ya bayyana wasu dalilan sa da yasa ya yi wakar sa ta 'Ta leko ta labe'

A wata hira da yayi da 'yan jarida, fitaccen mawakin yayi bayani kamar haka:

Ka yi wa Ganduje waka kuma ya ci zabe, ya ka ji?

Alhamdulillahi haka mu ke farin ciki dari bisa dari ko kuma na ce dari bisa miliyan na zuwan gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje karo na biyu a jihar Kano.

Kahutu Rarara: Dalilin da ya sa nayi wakar 'Ta leko ta labe'
Kahutu Rarara: Dalilin da ya sa nayi wakar 'Ta leko ta labe'
Asali: Facebook

Za ka iya karin bayani kan wakarka ta leko ta labe?

Abin da ya faru shine, wadanda su ke ikirarin sun samu nasara da magudi da cuce, sai Allah ya tona musu asiri. Suna ta ihu suna murna, suna ta fasa gidaje da ofishin mutane, suna bin mutane suna duka suna cewa sun ci zabe. Da su ka yi wannan murna, aka dakatar da zabe, sai na je na yi wakar 'ta leko ta labe', kuma gashi cikin ikon Allah, Allah ya tabbatar mana da nasara.

KU KARANTA: Najeriya na bukatar N10trn don habaka tattalin arziki - Fashola

Akwai sabuwar wakar da ka shirya ta nasarar Ganduje?

Ita ce wadda na ke mata take da, "ba da mu ta bare ba."

Kana yawan ambatar tsula, wai waye wannan tsulan?

Wannan ai harbin iska ne, kasan riga ce idan ka dinka babu wuya, duk wanda ya zo ya gani idan ta yi masa to shi ya janyowa kansa. Ba duka ba kama suna, saboda in za ka yi a baya akwai tsulolin dayawa in ka auna, wanda ya dau rigar ya maka a wuyanshi to shi ya maka.

Yanzu dai mun ce dan karen tsula da tsula, sai ku sake shiri "Ganduje ya koma magudin ku bai yi nasara ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel