Zaben cike gurbi: Masana'antar Kannywood ta taya gwamna Ganduje murnar samun nasara

Zaben cike gurbi: Masana'antar Kannywood ta taya gwamna Ganduje murnar samun nasara

Dandalin masana'antar Kannywood ta fina-finan Hausa, ya taya gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, murnar samun nasara ta lashe zaben gwamnan jihar Kano karo na biyu da aka gudanar a ranar Asabar, 23 ga watan Maris.

Mun samu cewa, dandalin masana'antar Kannywood ta fina-finan Hausa, ta yi tarayya da jam'iyyar APC wajen taya gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Ganduje, murnar samun nasarar tazarcen kujerar sa a karo na biyu.

Zaben cike gurbi: Masana'antar Kannywood ta taya gwamna Ganduje murnar samun nasara
Zaben cike gurbi: Masana'antar Kannywood ta taya gwamna Ganduje murnar samun nasara
Asali: Depositphotos

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, wasu daga cikin fitattun jaruman Kannywood sun taya gwamna Ganduje murnar samun nasara ta hanyar watsa sakonni a shafukan su na zaurukan sada zumunta.

Ire-iren mashahuran jaruman Kannywood da suka taya gwamna Ganduje murnar samun nasara a shafukan su na dandalan sada zumunta sun hadar Ali Nuhu, Fati Shu'uma da kuma Baban Chinedu duk cewar ba ya da wata alkibla ta akidar siyasa.

Gwamna Ganduje ya sha da kyar yayin lallasa babban abokin adawar sa na jam'iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf, inda ya ba shi tazara ta kimanin kuri'u 8,982 kacal kamar yadda hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta watau INEC ta bayyana.

KARANTA KUMA: Ba za mu bari jam'iyyar adawa ta kusanci jagoranci ba a Majalisar tarayya - Oshiomhole

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, dandalin Kannywood ya yi tarayya da wasu daga cikin al'ummar jihar Kano wajen taya gwamna Ganduje murnar samun nasarar tazarce yayin babban zaben da aka gudanar a karshen makon da ya gabata.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel