PDP ta lashe zaben cike-gibi na ‘Yan Majalisar Adamawa da Taraba

PDP ta lashe zaben cike-gibi na ‘Yan Majalisar Adamawa da Taraba

Hukumar zabe mai zaman kan-ta a Najeriya watau INEC ta sanar da cewa jam’iyyar PDP ce tayi nasara a zaben kujerar ‘yan majalisar dokoki a mazabun da su ka rage a jihohin Adamawa da Taraba.

Jam’iyyar hamayya ta PDP ce ta lashe zaben cike-gurbi da aka yi a yankin Uba/Gaya da ke jihar Adamawa. Haka kuma PDP ce ta ci zaben da aka yi a mazabar Nassarawo Binyeri. Yanzu dai APC ta rasa wadannan kujeru.

Malamin zaben na Uba Gaya watau Dr. Adedeji Ahmed na jami’ar fasaha ta Modibbo Adama de ke Garin Yola (MAUTECH), ya sanar da cewa Abbas Aminu Iya na PDP ya doke ‘dan takarar APC watau Mohammed Hayatu Atiku.

KU KARANTA: APC ta ce sam ba ta yarda da zaben Gwamna da aka yi a Sokoto ba

PDP ta lashe zaben cike-gibi na ‘Yan Majalisar Adamawa da Taraba
PDP ta lashe kujerun da su ka rage a Adamawa da Taraba
Asali: Facebook

Haka zalika Malamin zaben da yayi aiki a cikin mazabar Nassarawo Binyeri watau Dr Sulaiman Zarma na FCE Yola ya tabbatar da cewa ‘dan takarar PDP Umar Nashon Gubi ya doke Mahmud Dabo a zaben majalisar dokokin jihar.

INEC ta shirya zabe a yankin Nassarawo Binyeri ne bayan ‘dan takarar jam’iyyar APC watau Adamu Kwanate ya rasu ana daf da zaben bana. Marigayi Adamu Kwanate shi ne yake kan kujerar kuma yake neman tazarce kafin ya cika.

A jihar Taraba, PDP ce ta lashe zaben cike-gibin da aka yi. PDP ce ta kawo kujerar majalisar dokoki na yankin Ussa da kuma Ardo Kola na jihar. Timothy Anderifun da Dominic Bukuni ne su ka samu nasara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel