Tambuwal ya sake lashe zaben gwamna a jihar Sokoto
Labarin da Legit.ng ta samu yanzu-yanzun nan ya tabbatar ma ta da cewar gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya sha fda kyar bayan ya lashe zaben gwamnan jihar Sokoto da banbancin kuri'un da ko 400 basu kai ba.
A baya Legit.ng ta kawo maku labarin cewar a jihar Sokoto dai jam'iyyar PDP ce ke kan gaba da kuri'u 3,412 a zaben ranar 9 ga watan Maris. A yau kuma za a gudanar da zabe a mazabu 135 a kananan hukumomi 22 na jihar inda ake sa ran mutane 75,403 za su kada kuri'a.
Labari ya zo mana daga Jaridar Daily Trust cewa an zo gaf-da-gaf tsakanin jam’iyyar APC da kuma PDP a jihar Sokoto inda Gwamna mai-ci watau Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal yake neman tazarce.
Zaben cike-gibin da aka yi jiya, yayi wa Aminu Waziri Tambuwal illa matuka inda sakamakon zaben da aka fitar ya nuna cewa ‘Dan takarar APC Alhaji Ahmed Aliyu ya samu nasara sosai a zaben da aka karasa jiya.
Gwamna Aminu Tambuwal na PDP yana da kuri’u 489,558 yayin da ‘Dan takarar APC Aliyu Ahmed ya samu kuri’a 486,145 a sakamakon da aka fitar a karon farko. A wancan lokaci Tambuwal ya bada ratar kuri'a 3, 413.
A zaben na cike-gibi da aka yi jiya, APC ta samu kuri’u 18, 342, inda jam’iyyar PDP mai rike da jihar ta ke baya da kuri’a 16, 987. Hakan na nufin jam’iyyar APC ta ba gwamna Tambuwal tazarar kuri’a 1, 355 a zaben na jiya.
Sakamakon da aka fitar kawo yanzu ya tabbatar da cewa APC ta yi nasara a kananan hukumomi 14, yayin da PDP ta lashe zaben kananan hukumomi 7 rak. Yanzu dai ana jiran sakamakon karamar hukumar Kebbe.
Karamar hukumar Sokoto ta Kudu
APC 313
PDP 278
Karamar hukumar Yabo
APC: 110
PDP: 106
Karamar hukumar Gwadabawa
APC 187
PDP 163
Karamar Tureta
APC 56
PDP 238
Karamar Kware
APC 211
PDP 186
Mazabar Katta Hakimii a karamar hukumar Illela
PDP-198
APC- 149
Mazabar Labuda /Gidan Taraminiya, akwati ta 005
PDP-102
APC-57
Mazabar Gidan Baiti, karamar hukumar Gwadabawa
PDP-97
APC -85
DUBA WANNAN: Kotu ta bayyana yadda INEC ta canja sakamakon zaben gwamna a Osun
Mazabar Gidan kolodo, karamar hukumar Kware
PDP – 185
APC -211
Karamar hukumar Bodinga, akwati ta 011
APC: 232
PDP: 256
Mazabar Bello Issa, akwati ta 012, karamar hukumar Sokoto ta Kudu
APC 187
PDP 133
Akwati ta 004, Mazabar Waziristan 'B', karamar hukumar Sokoto ta Arewa
APC 156
PDP 135
A yayin da ya rage saura karamar hukuma 1 a sanar da sakamakon zaben gwamna a jihar Sokoto, jam'iyyar PDP na da jimillar kuri'u Jimilla kuri'u 18342 daga mazabun da aka maimaita zabe, yayin da APC ke da adadin kuri'u 16987.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng