2019: Jam’iyyar APC ta zaftare tazarar PDP a Jihar Sokoto
Labari ya zo mana daga Jaridar Daily Trust cewa an zo gaf-da-gaf tsakanin jam’iyyar APC da kuma PDP a jihar Sokoto inda Gwamna mai-ci watau Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal yake neman tazarce.
Zaben cike-gibin da aka yi jiya, yayi wa Aminu Waziri Tambuwal illa matuka inda sakamakon zaben da aka fitar ya nuna cewa ‘Dan takarar APC Alhaji Ahmed Aliyu ya samu nasara sosai a zaben da aka karasa jiya.
Gwamna Aminu Tambuwal na PDP yana da kuri’u 489,558 yayin da ‘Dan takarar APC Aliyu Ahmed ya samu kuri’a 486,145 a sakamakon da aka fitar a karon farko. A wancan lokaci Tambuwal ya bada ratar kuri'a 3, 413.
KU KARANTA: APC ta doke PDP bayan an yi zaben cike-gibi a Jihar Filato
A zaben na cike-gibi da aka yi jiya, APC ta samu kuri’u 18, 342, inda jam’iyyar PDP mai rike da jihar ta ke baya da kuri’a 16, 987. Hakan na nufin jam’iyyar APC ta ba gwamna Tambuwal tazarar kuri’a 1, 355 a zaben na jiya.
Sakamakon da aka fitar kawo yanzu ya tabbatar da cewa APC ta yi nasara a kananan hukumomi 14, yayin da PDP ta lashe zaben kananan hukumomi 7 rak. Yanzu dai ana jiran sakamakon karamar hukumar Kebbe.
Hukumar INEC ta dage tattara kuri’un jihar har sai zuwa karfe 9:00 na yau da safe inda za a kawo kuri'un Kebbe.
Ga dai cikakken sakamakon da aka bayyana nan daga karashen zaben da aka yi jiya:
K/H APC PDP
Kware 211 186
Tureta 56 238
Isa 68 98
G/bawa 187 163
Yabo 110 106
D/Shuni 652 626
Sok Kudu313 278
Bodinga 299 309
Binji 517 1,039
Wurno 904 609
Wamakko 417 221
Rabah 1411 1319
Ilela632 607
Gudu 211 176
Silame 504 834
Sok Arewa 2212 1783
Shagari 242 263
Tambuwal 1392 1644
Sabon Birni 1023 887
Gada 5548 4336
Goronyo 1433 1265
Jimilla 18342 16987
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng