Kannywood: Mansurah Isah ta fadi abinda yafi janyo mutuwar a tsakanin ma'aurata

Kannywood: Mansurah Isah ta fadi abinda yafi janyo mutuwar a tsakanin ma'aurata

Mansurah Isah tsohuwar jaruma ce a Kannywood. Ta auri daya daga cikin tsaffin jiga-jigan jaruman Kannywood wato Sani Danja kuma a halin yanzu sun kai shekaru 11 suna tare.

A hirar da daily Trust tayi da ita, jarumar ta tabo batutuwa da dama da suka shafi Kannywood da ma sauran harkokin rayuwa.

Mansurah ta ce a halin yanzu dai ta dena fitowa a fina-finai sai dai hakan baya nufin ta wanke hannun daga Kannywood domin kuwa tana taka rawa a fannin rubutu da tsara fina-finai.

Ta kuma ce akwai wani sabon fim da suka shirya mai suna 'Buri uku a duniya' da zai fito nan da kwani goma. Ta ce yanzu tafi mayar da hankali ne a kan ayyukan tallafawa marasa galihu kuma mijinta yana matukar ba ta goyon baya.

DUBA WANNAN: El-Rufai ya bayyana abinda zai yiwa wadanda ba su zabe shi ba

Kannywood: Mansurah Isah ta fadi babban abinda yafi janyo mutuwar aure
Kannywood: Mansurah Isah ta fadi babban abinda yafi janyo mutuwar aure
Asali: Twitter

An yi mata tambaya a kan menene sirrin zaman lafiya a aure duba da cewa yawancin jaruman fina-finai aurensu bai cika dade wa ba amma gashi ita ta kwashe shekaru 11 a gidan mijinta?

Mansurah ta bayar da amsa kamar haka: "Mai gida na jarumi ne kuma kyakyawa mai kudi irin dai wanda mata suke so sai dai wasu lokutan dole in rika kawar da kai na daga wasu abubuwan duba da cewa addinin musulunci ya bashi damar auren mata hudu.

"Wani babban abu kuma shine kutse da yawancin mata suke yi a cikin wayoyin salular mazajensu. A duk lokacin da mace da fara bincike cikin wayar mijinta da leko abinda bai dace ta gani ba, abin zai dame ta kuma ya shafi aurensu.

"Amma idan mace tayi nesa daga wayar mijinta da komfutarsa da sauran abubuwansa tabbas za ta samu kwanciyar hankali kuma aurenta zai dore. Ina tunanin wannan sune dalilin da suka sanya aure mu ke cigaba da karfafa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel