PDP zata ja daga idan ba'a baiwa Abba Kabir Gwamnan jihar Kano ba

PDP zata ja daga idan ba'a baiwa Abba Kabir Gwamnan jihar Kano ba

- Jam'iyyar PDP ta nuna cewar ita ta lashe zaben jihar Kano

- Jam'iyyar ta bukaci hukumar zabe ta baiwa dan takarar ta kujerar gwamnan jihar

PDP ta nuna rashin amincewar ta a zaben jihar Kano, ta bukaci a baiwa Abba kujerar gwamna
Hoton dan takarar gwamnan jihar Kano a jam'iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf
Asali: Twitter

Babbar jam'iyyar adawa ta PDP, bukaci hukumar zabe mai zaman kanta, data bayyana dan takarar ta Abba K. Yusuf, a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna na jihar Kano.

Jam'iyyar tace dan takarar na ta ya samu kuri'u fiye da abokin hamayyar sa na jam'iyyar APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje.

KU KARANTA: Babu wani dalilin da zai sa a soke zaben Kano - APC ta yiwa PDP raddi

Sanarwar wacce ta fito daga bakin mai magana da yawun Jam'iyyar, Mista Kola Ologbondiyan, ya bayyana cewa babu wani sahihin zabe da aka gabatar a jihar a yau, wanda zai nuna cewa Ganduje ya lashe zaben.

Ya kara da cewa hukumar zabe ta san da cewar, 'yan ta'aaddan da jam'iyyar APC ta dauko su suka hana gabatar da zabe a yankuna da dama a jihar ta Kano.

Yace: "Kowa ya san da cewar al'ummar sun riga sun nuna zabinsu shine dan takarar jam'iyyar mu ta PDP, wato Abba K. Yusuf. Saboda haka duk wani yunkuri na murde wannan zabe zai iya kawo rikici ga al'umma. "

Saboda haka muna kira ga hukumar zabe data tabbatar da tayi abin da ya dace da al'ummar jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel