Sokoto: Kusoshin jam'iyyun APC da PDP sun janyo tashin tarzoma a rumfar zabe

Sokoto: Kusoshin jam'iyyun APC da PDP sun janyo tashin tarzoma a rumfar zabe

Rikici ya barke tsakanin wasu jiga-jigan jam'iyyar APC da PDP a rumfar zabe mai lamba 005 da 009 da ke Magajin Gari, Ward 'B' shiyyar Danfarijo a yayin da ake gudanar da zabe a yau Asabar.

Jiga-jigan 'yan siyasan sunyi kokarin nuna iko da isa ne wadda hakan ya janyo tashin hankali a zaben da ake gudanarwa na cike gibi a karamar hukumar Sokoto ta Arewa.

'Yan siyasan dai sune Alhaji Murtala Daniya na jam'iyyar PDP da tsohon shugaban karamar hukumar Sokoto ta Arewa na APC, Alhaji Abdullahi Hassan da shugaban matasa na APC, Nasiru Italiya.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ta ruwaito cewa Daniya na jam'iyyar PDP ne ya daga kuri'arsa ya nuna wa al'umma bayan ya dangwale wanda hakan ya janyo wasu suka fara watsa masa kasa da jifansa da ma'aikatan INEC da jami'an tsaro.

DUBA WANNAN: Sule Lamido ya fadi yadda APC da Kwamishinan 'yan sanda suka yiwa PDP magudin zabe

Sokoto: Rikici ya barke tsakanin jiga-jigan APC da PDP a rumfar zabe
Sokoto: Rikici ya barke tsakanin jiga-jigan APC da PDP a rumfar zabe
Asali: Twitter

Daga bisani dole sai da aka karo jami'an tsaro kuma 'yan sanda su kayi amfani da barkonon tsohuwa wurin kwantar da tarzomar da ta janyo aka dakatar da zaben na kusan sa'o'i uku.

Jami'in zaben, Mr Otu Cassius ya shaidawa NAN cewa sun iso rumfar zaben tun karfe 7 na safiya kuma an fara tantance masu zabe da kada kuri'a nan take ba tare da bata lokaci ba saboda na'urar card reader tana aiki.

Cassius, wanda dan yiwa kasa hidima ne ya ce komi na tafiya yadda ya kamata kafin afkuwar rikicin.

Wani jami'in PDP mai suna Alhaji Bashiru Abdulkadir ya shaidawa NAN cewa ba laifi bane nuna wa al'umma takardan kuri'a domin a san wanda ya zaba domin ko shugaban kasa ya yi hakan a lokacin zaben shugabancin kasa.

Sai dai, jami'in APC, Muntari Mohammed bai amince da hakan ba inda ya ce hakan ya sabawa dokokin zabe kuma ya ce zai shigar da kara ga hukuma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel