‘Yan bindiga sun kashe dan sanda 1, sun sace 6 a mahakar zinare a Zamfara

‘Yan bindiga sun kashe dan sanda 1, sun sace 6 a mahakar zinare a Zamfara

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kashe jami’in dan sanda tare da sace wasu mutane 6 a mahakar zinare da ke kauyen Sunke a karamar hukumar Anka, jihar Zamfara, kamar yadda jaridar daily Trust ta rawaito.

‘Yan bindiga sun dade suna kai hare-hare a mahakar zinare dake sassan jihar Zamfara.

Ko a watan Nuwamba na shekarar 2016 sai da wasu ‘yan bindiga suka kasha mutane 42 a wurin hakar zinare dake kauyen Bindin a karamar hukumar Maru.

Shugaban karmar Anka, Alhaji Mustapha Gado, ya shaida wa majiyar Legit.ng ta wayar tarho cewar ‘yan bindigar sun kai hari mahakar zinaren inda suka kashe jami’in dan sanda tare da sace mutane 6.

‘Yan bindiga sun kashe dan sanda 1, sun sace 6 a mahakar zinare a Zamfara
Jami'an 'yan sanda
Asali: Twitter

Ya ce an tura ‘yan sanda wurin ne domin tabbatar da tsaro a wurin hakar zinaren amma ‘yan bindigar su ka ki ma su farmaki. Sai dai, ya bayyana cewar ‘yan bin digar sun sako jami’an ‘yan sanda 6 da suka sace amma sun kwace bindigun su.

DPO na karama hukuma ya fada min cewar an sako jami’an ‘yan sandan amma ‘yan bindigar sun kwace ma su bindigun su,” cewar sa.

Sannan ya cigaba da cewa, “mun shawarci hukuma a kan a rufe wuraren hakar zinaren amma har yanzu bakin haure da suka kafa injina na cigaba da harkokin su.

DUBA WANNAN: Dalilin da ya sa Abba da Kwankwaso suka fasa ziyarar mazabar Gama

Mun tuntubi hukumomin da abin ya shafa kuma sun bamu iznin rufe wuraren hakar zinaren

“Amma da muka basu takardar su kwashe kayansu daga wurin sai suka nemo jami’an tsaro domin sub asu kariya.

Kokarin jin ta bakin SP Muhammad Shehu, kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Zamfara, a kan afkuwar lamarin bai samu ba har zwa lokacin da aka wallafa rahoto.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel