Raba gardama: INEC ta fitar da adadin akwati da mazabun da za a sake zabe a Bauchi

Raba gardama: INEC ta fitar da adadin akwati da mazabun da za a sake zabe a Bauchi

Ofishin hukumar zabe ta kasa (INEC) da ke jihar Bauchi ya bayyana cewar za a gudanar da zaben gwamna na raba gardama a kananan hukumomi 15 da aka soke sakamakon zabe.

Kwamishinan zabe a jihar Bauchi, Ibrahim Abdullahi, ne ya sanar da haka a yau yayin gana wa da manema labarai.

A cewar sa, za a maimaita zaben ne a akwati 36 da ke mazabu 29 a kananan hukumomi 15 da abin ya shafa. Adadin ma su rijistar zabe 22,759 ake sa ran zasu kada kuri'a a zaben.

A wani labarin na Legit.ng mai nasaba da wannan, kun ji cewar hukumar zabe ta kasa mai zaman kan ta (INEC) ta bayyana cewar zata cigaba da tattara wa da sanar da sakamakon zaben gwamna a jihar Ribas a ranakun 2 da 5 ga watan Afrilu.

Raba gardama: INEC ta fitar da adadin akwati da mazabun da za a sake zabe a Bauchi
Gwamnan Bauchi yayin kada kuri'a a zabe
Asali: Twitter

Hukumar ta sanar da cewar idan da bukatar sake yin zaje a wasu mazabu, zata tu hakan ranar 13 ga watan Afrilu sannan ta bayar da takardar shaidar samun nasara a zabe ranar 19 ga watan Afrilu.

DUBA WANNAN: Ba zan saka baki a zabukan da za a maimaita ba – Sakon Buhari ga APC

Festus Okoye, kwamishinan sashen yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a, ne ya sanar da hakan yayin jawabi ga manema labarai a Abuja.

A cewar sa, hukumar INEC ta dauki matakan taka wa kotu birki don ganin ba ta hana ta cigaba tattara wa da sanar da sakamakon zaben a kananan hukumomin da aka samu matsala ba

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel