Kano: Na hannun daman Atiku ya kare shi a kan goyon bayan Abba Gida-Gida

Kano: Na hannun daman Atiku ya kare shi a kan goyon bayan Abba Gida-Gida

Dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya ce zai yi duk mai yiwuwa domin ganin dan takarar gwamnan jam'iyyar PDP na jihar Kano, Abba Kabiru Yusif ya kai ga samun nasara kamar yadda hadiminsa Alhaji Mohammed Abdullahi Sugar ya bayyana.

Sugar ya yi wannan furucin ne a lokacin da ya ke mayar da martani a kan rahotonin da ke nuni da cewa Atiku ya yi watsi da Abba.

Yusuf zai fafata da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje mai ci a yanzu a zaben karashe da Hukumar Zabe mai Zaman Kanta, INEC za ta gudanar a ranar Asabar mai zuwa.

DUBA WANNAN: Rarara ya yi karin haske a kan rahotannin kai masa hari

Kano: Atiku zai yi duk mai yiwuwa domin Abba ya yi nasara - Hadiminsa
Kano: Atiku zai yi duk mai yiwuwa domin Abba ya yi nasara - Hadiminsa
Asali: UGC

"Wannan karya ce kawai da ake kirkiro domin a bata wa Atiku suna; ba a taba samunsa da yiwa jam'iyya zagon kasa ba a tsawon lokacin da ya ke siyasa," inji Sugar.

"Atiku shine shugaban kasarmu mai jiran gado kuma yana goyon bayan takarar Abba saboda bayan Adamawa, Kano ce gidansa. Muna murna saboda al'ummar Kano sun waye a siyasa, hakan yasa ba su zabi jam'iyyar APC ba," inji Sugar a hirar wayar tarho da akayi dashi.

Sugar wanda kwareren dan siyasa ne a Kano ya ce Abba sai kawo sauyi mai amfani a Kano idan ya zama gwamna.

"A karkashin mulkin Abba, Kano za ta dawo da martabarta a matsayin cibiyar kasuwanci a Arewa. Harkokin kasuwanci za su habbaka kuma jihar za ta cika da harkokin arziki na rayuwa. Kwankwaso ba zai rika juya shi ba kamar yadda wasu ke hasashe," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel