Rarara ya yi karin haske a kan rahotannin kai masa hari

Rarara ya yi karin haske a kan rahotannin kai masa hari

Shararren mawakin siyasa kuma Shugaban harkokin waka a kwamiti mai goyon bayan zarcewar shugaban kasa Buhari a zaben 2019, Dauda Kahutu Rarara ya musanta rahotannin da ke yaduwa na cewa an kai masa hari.

A hirar wayan tarho da Rarara ya yi da wakilin Daily Trust ya ce, "bani da masaniya a kan wannan labarin."

An fara yada jita-jitan ne a daren ranar Talata inda aka ce wasu 'yan bindiga da ba san ko su wanene ba sun kaiwa mawakin hari a dakin sarrafa wakansa da ke Zoo Road a Kano.

Labarin ya ce ta kyar mawakin ya tsira da ransa kafin 'yan bindigan sun bankawa studio dinsa wuta.

"Wannan labarin duk karya ne," inji shi.

DUBA WANNAN: Har yanzu muna tattaunawa da wadanda ke garkuwa da Sheikh Sulaiman - Iyalansa

Rarara ya yi karin haske a kan rahotannin kai masa hari
Rarara ya yi karin haske a kan rahotannin kai masa hari
Asali: Facebook

"Bani da masaniya a kan labarin. Bashir, shin kai bako ne a Najeriya ko Kano? Mutane masu muggun nufi sun saba yada labaran karya a game da ni.

"Sun ce wai na mutu, sun ce nayi hadari har an yanke min hannu da kafa; sun ce an kone gida na saboda nayi wakar da ba ta yiwa Kwankwaso da Shekarau dadi ba. Wannan ba sabon abu bane. Dul karya ne," inji shi.

Mawakin ya ce lafiyarsa kalau ba abinda ya same shi.

"Ina nan safiya ta kalau. Yanzu haka ina cikin studio ina tsara wakar da na ke yiwa Gwamna Abdullahi Ganduje da za ayi amfani dashi a mazabar gama inda za a gudanar da zabe a ranar Asabar mai zuwa," inji Rarara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel