Lalatacen maigida: Miji ya kai karar matarsa kotu a kan yawan jigbansa da ta ke yi

Lalatacen maigida: Miji ya kai karar matarsa kotu a kan yawan jigbansa da ta ke yi

Wani dan kasuwa da ke zaune a garin Ibadan mai suna Oluwatosin Bakare ya shaidawa kotun unguwar Ile-Tuntun da ke zamanta a Mapo a Ibadan cewa a raba aurensa da matarsa Enitan saboda ta saba yi masa duka.

Bakare da ke zaune a Labo Owo a unguwar Dubge na garin Ibadan ya shaidawa alkali cewa yawan dukansa da barazanar kashe shi ne dalilin da yasa ya ke rokon kotun da raba aurensa da matar.

Na gaji da dukan da mata ta take min- Mai gida ya fadawa kotu
Na gaji da dukan da mata ta take min- Mai gida ya fadawa kotu
Asali: Twitter

"Rashin binciken da banyi ba kafin in aure Enitan shine dalilin da yasa na shiga halin da na ke a yanzu.

"Ranka ya dade, tunda Enitan ta shigo gida na sai halayenta suka canja na kasa gane kanta. Sau da yawa ba ta min biyaya game da harkokin cikin gidan mu.

DUBA WANNAN: Har yanzu muna tattaunawa da wadanda ke garkuwa da Sheikh Sulaiman - Iyalansa

"Na yi kokarin sanar da Faston mu domin ya yi mata nasiha ta canja amma hakan bai warware matsalar ba. Halayen ta sun kara kazanta ne bayan Faston ya yi mata nasiha.

"A wata rana cikin watan Oktoban 2018, Enitan ta taba sharara min mari lokacin da na shiga dakin mu, sannan ta ciro wuka domin ta daba min.

"Da kyar dai na tsira ba tare da ta yi min rauni ba.

"Ba zan iya kirga adadin lokutan da ta ke kai min hari a cikin mutane tana yaga min kaya a coci da wasu wuraren ba.

"Wasu lokutan idan nayi latin dawowa gida daga aiki, Enitan za ta kallubalance ni wasu lokutan ta doke ni.

A bangarenta, Enitan ta ce ba ta son a raba auren duk da cewa ba ta musanta wasu daga cikin zargin da Oluwatosin ya gabatar a kanta ba.

"Ranka ya dade, faston mu shine ke kawo cikas a aure na da Oluwatosin.

"Faston mu ne ya bawa mijina shawarar ya auri wata mata daga cocinsa.

"Na lura halayen mijina sun canja tun lokacin da nayi bari. Ya dena kulawa da ni kuma ya fara dawowa gida cikin dare."

Alkalin kotun, Cif Henry Agbaje ya bukaci ma'auratan sun gabatar da hujoji domin tabbatar da zargin da suka yiwa juna.

Ya kuma dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 4 ga watan Afrilu kuma ya bukaci su kawo 'yan uwansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel