Tabarbarewar ilimi a Najeriya: Kalli yadda wasu daliban Firamari suke daukan darasi
Sanannen lamari ne cewa ilimi a Najeriya na cikin mawuyacin hali, tun daga matakin farko na Firamari har zuwa matakin karshe na jami’a, babu inda aka sha, inda zaka tarar da matsalar dake damun firamari tana damun hatta jami’a.
Don haka tasa yan Najeriya ke yawan yin kiraye kiraye ga gwamnatocin tarayya, jahohi da na kananan hukumomi da nufin su zage damtse ko a iya fidda A’I daga rogo, maganar gaskiya shine wasu shuwagabannin gwamnati suna kwatantawa, amma fa wasu ko a jikinsu, wai an tsikari kakkausa.
KU KARANTA: Rayuwata na cikin hadari don Allah ku taimakeni – Inji Alaramma Ahmad Sulaiman
Ana cikin wannan hali na tangal tangal a banaren ilimi ne sai kwatsam Legit.ng ta ci karo da wata makarantar Firamari dake jahar Abia, wanda halin da makarantar take ciki yasa yan Najeriya da dama sun bayyana bacin ransu tare da tofa tofin Allah tsine.
Ita dai wannan makaranta bata da ofis ko guda daya da Malamai zasu yi amfani dashi, bata da dakin karatu, kuma bata da makewayi, azuzuwa da dama sun fadi, azuzuwan da suka rage kuma rufinsu ya lalace haka dalibai suke zama a kasa suna daukan darasi.
Wannan matsala bata kebantu da jahar Abia kadai ba, matsala ce data mamaye jahohin Najeriya gaba daya, ba zaka rasa irin wannan makaranta a kowanne jaha daga cikin jahohin Najeriya 36 ba, hatta a babban birnin tarayya ba zaka rasa irin wannan makaranta ba.
Idan zaku tuna a makon data gabata ne bidiyo wata karamar yarinya ya dinga yawo bayan an sallameta daga makaranta saboda bata biya kudin jarabawa ba, inda take korafin cewa bai kamata a koreta ba, kamata yayi Malamarta ta bugeta, ta kyaleta ta zauna a makaranta.
Wannan lamari ya faru ne a garin Sapele, sakamakon wannan bidiyo tasa gwamnan jahar Delta, ya shiga cikin maganar, inda tuni ya dakatar da shugabar makarantar, sa’annan ya bada kwangilar gyara makarantar, ita kuwa yarinyar ta samu tallafin makudan kudade daga manyan mutane daban daban.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng