APC ta yabawa matakin da INEC ta dauka a zaben Jihar Bauchi

APC ta yabawa matakin da INEC ta dauka a zaben Jihar Bauchi

Labari ya zo mana daga jaridar Daily Trust cewa jam’iyyar APC na bangaren jihar Bauchi, tayi murna da matakin da hukumar zabe ta dauka a game da zaben gwamna na jihar a Ranar Talata 19 ga Watan Maris.

Shugaban Jam’iyyar APC mai mulki a jihar Bauchi, ya bayyanawa manema labarai cewa sun yi matukar jin dadin bin umarnin babban kotun tarayya da hukumar zabe na kasa na INEC tayi na dakatar da sanar da zaben gwamnan jihar.

Alhaji Uba Ahmed Nana yake cewa abin da ya kamata kenan INEC ta bi umarnin da kotu ta bada na cewa ka da a cigaba da tattara kuri’un da aka kada a karamar hukumar Tafawa Balewa a zaben gwamna da aka yi kwanakin baya.

KU KARANTA: INEC za ta kalubalanci hukuncin da aka yanke game da zaben Bauchi

APC ta yabawa matakin da INEC ta dauka a zaben Jihar Bauchi
APC ta fadawa INEC cewa tayi daidai na fasa sanar da zaben Bauchi
Asali: Twitter

Kotu tace cigaba da kididdiga kuri’un yankin Tafawa Balewa ya sabawa dokar zabe na 2010 da aka yi wa kwaskwarima. Yanzu haka jam’iyyar APC tana bayan PDP mai adawa ne kamar yadda sakamakon da aka sanar kawo yanzu ya nuna.

Shi kuma shugaban PDP na Bauchi, Alhaji Hamza Koshe Akuyam, yace ba su ji dadin wannan mataki da kotu ta yanke ba. Koshe Akuyam yace wannan sabon umarni da Alkalai su ka yanke ya ci karo da ra’ayin mutanen Bauchi.

Shugaban jam’iyyar hamayyar yace sun ci zaben gwamna da aka yi hankali kwance a kowace karamar hukuma da mazaba. Jam’iyyar tayi kira ga Mabiyan ta da su kwantar da hankalin su tare da gujewa duk abin da zai kawo rikici.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel