Hako fetur: Mun kusa cin ma rabin aiki a Jihar Bauchi - Inji Maikanti Baru

Hako fetur: Mun kusa cin ma rabin aiki a Jihar Bauchi - Inji Maikanti Baru

Mun ji labari, kamfanin man fetur na Najeriya watau NNPC ta bayyana cewa aikin da aka soma na hako danyen man fetur a jihar Bauchi da ke cikin Arewa maso gabashin Najeriya yayi nisa kawo yanzu.

Shugaban kamfanin NNPC, Maikanti Baru, ya bayyana cewa an haki kusan taku 6, 700 a rijiyar man Kolmani – River na II. An dai kaddamar da wannan aikin a watan jiya, a lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya je da kan sa.

Maikanti Baru yayi wannan jawabi ne ta bakin Kakakin kamfanin man na Najeriya watau Ndu Ughamadu. NNPC tace za a haki taku 14, 200 ne kafin a cin ma man fetur da kuma iskar gas a wannan sabuwar rijiyar mai ta Kolmani II.

KU KARANTA: An hana INEC sanar da wanda ya ci zaben Gwamna a Bauchi

Hako fetur: Mun kusa cin ma rabin aiki a Jihar Bauchi - Inji Maikanti Baru

Masu hako danyen fetur a Arewa maso Gabas sun kusa cin ma rabin aiki
Source: Depositphotos

Yanzu dai an kusa cin ma rabin aikin kamar yadda kamfanin NNPC din ta bayyana jiya. Maikanti Baru ya bayyana hakan ne a lokacin da wata kungiya ta PETAN masu sha’anin harkar man fetur ta ba sa wani babban kyauta a Birnin Abuja.

Daily Trust ta rahoto cewa Ma’aikatan man za su sanar da cewa ko an samu fetur a yankin yayin da su ka cigaba da yunkurin tono arzikin kasar. Wannan dai yana cikin shirin gwamnatin Buhari na hako danyen fetur a Arewacin Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel