NLC ta bawa FG zuwa watan Mayu ta fara biyan ma fi karancin albashi

NLC ta bawa FG zuwa watan Mayu ta fara biyan ma fi karancin albashi

Kungiyar kwadago (NLC) na son gwamnatin tarayya ta fara biyan sabon ma fi karancin albashi ga dukkan ma'aikata da ke fadin Najeriya kafin bikin ranar watan Mayu.

Mista Najeem Yasin , mukaddashin shugaban NLC, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a yau, Talata, a Abuja

Ya yaba wa majalisar dattijai bisa amincewar da ta yi da dokar mayar da ma fi karancin albashin ma'aikaci a Najeriya zuwa N30,000 a wata.

Tun kafin zabukan shekarar 2019 ne majalisar wakilai ta kasa ta amince da kudirin mayar da ma fi karancin albashi zuwa N30,000.

Tunda fari, kungiyar gwamnoni ta fara yin tayin biyan N24,000 a matsayin ma fi karancin albashi yayin da gwamnatin tarayya ta mika tayin biyan N27,000 ga zauren majalisar kasa.

NLC ta bawa FG zuwa watan Mayu ta fara biyan ma fi karancin albashi
NLC ta bawa FG zuwa watan Mayu ta fara biyan ma fi karancin albashi
Asali: Twitter

"Mun yaba wa majalisar dattijai bisa amincewar ta da dokar mayar da ma fi karancin albashin ma'aikata zuwa N30,000 amma har yanzu 'da sauran rina a kaba' don hankalin ma'aikata ba zai kwanta ba sai an fara biyan su ma fi karancin albashin.

DUBA WANNAN: Dalilin da ya sa har yanzu ba mu biya ma’aikatan wucin gadi ba – INEC

"Duk da ma'aikatan Najeriya sun ji dadin abinda majalisar dattijai ta yi, su na so 'yan majalisar su tabbatar da cewar an fara biyan ma'aikata sabon albashin da doka ta amince da shi.

"Mu na son gwamnatin tarayya ta tabbatar da fara biyan sabon albashin kafin ranar bikin watan Mayu, ranar da ake bikin 'ranar ma'aikata'. Abinda ya dace gwamnati ta yiwa ma'aikaci kenan a wannan rana mai muhimmanci," a cewar shugaban kungiyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel