PDP ta fadawa APC cewa ita za ta ci zaben da za a karasa kwanan nan

PDP ta fadawa APC cewa ita za ta ci zaben da za a karasa kwanan nan

- Jam’iyyar PDP tace tana da yakinin cewa za ta lashe zabukan da za a karasa

- Jam’iyyar adawar na da tabbacin samun nasara a duka Jihohin da su ka rage

- PDP tace Gwamnatin APC ta jawo tashin hankali sannan ta koma ta na kuka

Babbar jam’iyyar hamayya a Najeriya, PDP, ta bayyana cewa ita ca za ta lashe zabukan gwamna da su ka rage a kasar. Sakataren yada labarai na jam’iyyar adawar, Mista Kola Ologbcodiyan, shi ne ya bayyana mana wannan.

A jawabin da Kola Ologbcodiyan ya fitar a jiya Lahadi, 17 ga Watan Maris, ya bayyana cewa jam’iyyar APC za ta sha kasa a zabukan da za a karasa a wasu jihohin kasar. PDP tace ta riga ta hango nasarar ta a zaben kasar.

KU KARANTA: Abin da ya hana Kwankwaso da mutanen sa kama barayin akwati

PDP ta fadawa APC cewa ita za ta ci zaben da za a karasa kwanan nan
Jam'iyyar PDP tace ita za ta ci zaben gwamna a Kano, Bauchi, Sokoto da Adamawa
Asali: Twitter

Jam’iyyar adawar ta kuma zargi APC da kokarin murde zabukan da ake yi tare da amfani da jami’an tsaro wajen yi wa ‘yan adawa barazana, da kuma yunkurin kawo rashin zaman lafiya a lokacin zabe domin yin magudi.

Duk da haka, PDP tace jam’iyyar APC ta na yi wa Duniya kukan karya kamar ba ita ba ce ke kokarin amfani da iko wajen tafka magudin zabe ba. PDP tace kuri’un da aka kirga ya nuna cewa su ne ke kan gagarumar nasara.

Jam’iyyar ya PDP tace APC ta komawa tada rikici a Ribas, yayin da kuma tace jama’a sun guji jam’iyyara mai mulki a Kano. Kola Ologbcodiyan ya kuma ce PDP ta ci zaben gwamna a jihohin Sokoto, Adamawa da Bauchi ta gama.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel