Garkuwa: Ana neman Iyalin Ahmad Sulaiman su fito da N300m

Garkuwa: Ana neman Iyalin Ahmad Sulaiman su fito da N300m

Wadanda su ka sace babban Alaranman nan na kungiyar Izala a Najeriya watau, Ahmad Sulaiman Ibrahim, su na neman a biya makudan kudi kafi su saki wannan Malamin inji jaridar Prime Times News.

Kamar yadda labari ya zo gare mu dazu, wadanda su ka sace wannan Alaranma, su na so a biya Naira Miliyan 300 idan har ana so a sake Malamin da kuma wasu mutum 5 dabam da aka sace tare da shi a Ranar Alhamis da ta gabata.

An sace wannan Malami ne da kuma wasu mutum 5 a kan hanyar Sheme zuwa Kankara a cikin Jihar Katsina, a lokacin da su ke dawowa daga wajen wani taron kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah (JIBWS).

KU KARANTA: Ana tattaunawa da masu garkuwan da su ka sace Malamin addini

Garkuwa: Ana neman Iyalin Ahmad Sulaiman su fito da N300m
Sai an biya kudi kafin a saki Malamin addinin da aka sace
Asali: UGC

Wani na kusa da wannan Malamin, mai suna Ismail Bunyaminu ya bayyanawa ‘yan jarida cewa wadanan Miyagu sun sa masu kudi har Naira Miliyan 300 kafin su sake Malaman. Yanzu dai za ayi kokarin hada kudi domin ceto Shehin.

Masu garkuwa da mutanen sun lafta kudin ne ganin cewa mutane 6 su ka cafke. Ismail Bunyaminu yace Iyalin Malamin sun zauna game da lamarin inda su ke neman wadannan mutane su rage kudin da su ka sa a tattaunawar da ake cigaba da yi su.

Za ayi kokarin hada wannan kudi ne daga hannun shugabannin kungiyar Izala da kuma gwamnatin jihar Kano. Jami’an tsaro a na su bangare, sun ce ba su san da batun biyan kudi ba, amma sun yi alwashin ceto wadanan Bayin Allah.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel