An kama mafarauta 3 'yan Najeriya a Nijar

An kama mafarauta 3 'yan Najeriya a Nijar

An kama wasu mafarauta 'yan Najeriya gudu uku a Jamhuriyar Nijar da ke zargi da satan namun daji a daya daga cikin gandun dajin duniiya da ke yammacin Afirka.

Ana zargin mafarautan ne da yin farautar namun daji daga wani babban gandun daji da ya hada kan iyakar Jamhuriyar Nijar da Benin da Burkina Faso.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa an kama mafarautan ne a kudu maso yammacin Dosso a cikin motar daukan kaya biyu cike makil da hauren giwa, fatun maciji da kawunnan wasu dabobin daji da suka hada da Bauna da Birai.

DUBA WANNAN: Tirkashi: An nada Dino Melaye da Ortom wakilan zabe a zaben gwamna da za a maimaita

An kama mafarauta 3 'yan Najeriya a Nijar
An kama mafarauta 3 'yan Najeriya a Nijar
Asali: Twitter

Gwamnatin kasar Nijar ta ce an samu bindigogin farauta guda shida, kekunnan hawa da adduna masu yawa da wasu sinadarai tare da mafarautan yayin da aka kama su.

Gwamnan jihar Dosso, Moussa Osusmane ya yabawa jami'an gandun dajin da suka kama mafarautan.

Gandun dajin mallakar majalisar Dinkin Duniya mai girman sakwaya kilomita 10,000 yana kunshe da namun daji daban-daban masu yawa kuma wuri ne da dabobi ke zuwa domin su tsira daga mafarauta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel