Jama’a sun komawa Allah domin samun sa’a a karashen zaben Kano

Jama’a sun komawa Allah domin samun sa’a a karashen zaben Kano

Yayin da ake cigaba da shiryawa karashen zaben gwamna na jihar Kano a wasu rumfunan zabe a fadin jihar, mun samu labari cewa jama’a da dama a Kano sun komawa Allah a daidai wannan lokaci.

Bayin Allah da-dama sun shiga yin ayyukan ibada iri-iri domin ganin wanda su ke so, sun kai labari a zaben da za a kammala. Jaridu sun bayyana cewa mutane rututu sun soma cika masallaci da salloli na musamman na rokon Allah.

Mutane kan yi sallar Al-Qunut sun a rangadi addu’o’i da nufin wadanda su ke goyon baya su lashe zaben da za a kammala a karshen mako mai zuwa. A kan ji irin wadannan mutane su na tafe su na kiran sunayen Allah a cikin Birnin Kano.

Bayan masu yawo, su na zikirin “Hasbunalahu Wani’imal Wakil”, akwai kuma wanda su ka tattara, su ka sheka har masallacin Manzon Allah SAW na Madina a kasa mai tsarki inda su ke addu’a ga Allah ya ba ‘dan takarar su nasara a zaben gwamna.

KU KARANTA: Babban Kotun daukaka kara ta sake ba Abba Yusuf gaskiya

‘Yan kasuwa dai su na kirkiro Umrah ta musamman domin su yi addu’ar con zabe. Kano tana cikin jihohin da aka gaza kammala zabukan gwamna a Najeriya. PDP ta samu kuri’u 1,014,353 yayin da APC mai mulki ta samu kuri’a 953,522 a zaben.

Wadannan ‘yan kasuwa sun dauki nauyin sufuri da jigilar masu zuwa kasa mai tsarki yi wa ‘yan siyasar addu’a. Haka kuma wasu su kan yanka rakuma, da shanu da kuma awaki don kurum su kai ga samun nasara a zaben da za ayi Ranar Asabar.

A halin yanzu dai Gwamna mai-ci Abdullahi Ganduje yana kokarin ganin ya koma kan mulki inda yake fuskantar barazanar gaske daga wajen Injiniya Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar PDP mai adawa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel