Kwankwaso ya magantu a kan maimaita zaben gwamna a Kano

Kwankwaso ya magantu a kan maimaita zaben gwamna a Kano

Jigo a jam'iyyar PDP reshen jihar Kano kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce sun gama shiri tsaf domin tunkarar zabe da hukumar INEC za ta maimaita a wasu yankunan jihar ta Kano a ranar 23 ga watan Maris na 2019 duk da cewa ba su gamsu da matakin hakan ba.

Kwankwaso ya ce ko da sau 100 za ayi zaben, dan takarsu Abba Yusif ne zai lashe zaben duba da yadda lamara ke tafiya a jihar. Ya ce za su dauki dukkan matakan da ya dace domin ganin sun lashe zaben kamar yadda Bbc ta ruwaito.

Kwankwaso ya magantu a kan maimaita zaben gwamna a Kano
Kwankwaso ya magantu a kan maimaita zaben gwamna a Kano
Asali: UGC

Ya ce, "Za mu dauki matakanmu ne bisa tsarin doka da oda da kotu, domin tabbatar da cewa an zauna lafiya a jihar Kano, kuma ba a kyale tinkiya ta haifi kare ba".

DUBA WANNAN: Tirkashi: An nada Dino Melaye da Ortom wakilan zabe a zaben gwamna da za a maimaita

Sanata Kwankwaso ya shawarci shugabanni na yanzu suyi koyi da mazan jiya kamar Marigayi Muhammadu Abubakar Rimi wanda akayi zabe ya sha kaye zai yi kashi na biyu amma ya hakura. Ya kuma bayar da misali da kansa a lokacin da ya nemi tazarce a matsayin gwamnan Kano ya sha kaye amma ya hakura.

Ya ce hankalinsu kwance ya ke dangane da zabukan da za a sake a wasu sassa na jihar domin su sun san cewa sun riga sun lashe zabe.

Tsohon gwamnan na jihar Kano ya koka a kan abinda ya kira zalunci da akayi a zaben na ranar 9 ga watan Maris saboda a cewarsa dokar da hukumar INEC tayi amfani da shi a zaben jihar Ogun ya sha banban da wanda akayi amfani da shi a Kano.

Ya ce dokar da INEC ta ce idan adadin kuri'un da dan takara na daya ya samu ba su kai yawan kuri'un da aka soke ba, to sai an maimaita zabe. Sai dai ya ce ba haka aka aikata a jihar Ogun ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel