Magidanci ya fadawa kotu dalilin da yasa yake yiwa matarsa duka

Magidanci ya fadawa kotu dalilin da yasa yake yiwa matarsa duka

A yau Juma'a ne wata kotun da ke zamanta a Mapo a garin Ibadan ta raba aure tsakanin wani direban motar haya Oluwole Kolapo da mai dakinsa Temitope saboda ba bu sauran soyaya a auren.

Shugaban kotun, Cif Ademola Odunade ya yanke hukuncin inda ya ce babu amfanin aure idan ba bu so da kauna tsakanin ma'auratan biyu.

Ya bawa mijin damar rike yaransu uku tunda sun rika sunn girma duba da cewar ya kwashe shekaru 25 tare da matarsa kafin su rabu.

Kafin a yanke hukuncin, Oluwole ya fadawa alkali cewa ya kasance yana dukan matarsa Temitope ne saboda bata masa biyaya.

Magidanci ya fadawa kotu dalilin da yasa yake yiwa matarsa duka
Magidanci ya fadawa kotu dalilin da yasa yake yiwa matarsa duka
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An kulla mikirci domin karya ni a siyasance - Okorocha ya yi korafi

A yayin da ya ke kare kansa daga zargin duka da neman mata a waje da ta ce ya keyi, Oluwole ya shaidawa kotu cewa matarsa kwata-kwata ba ta bin umurninsa shi yasa ke ya dukanta

"Da gaske ne cewa na doki Temitope amma saboda rashin biyaya da ta ke min yasa na aikata hakan.

"Ta saba bin bokaye da malaman tsibbu duk da cewa na gargade ta akan dena hakan.

"Rai na ya baci a lokacin da na gano layu da wasu magunguna a boye a dakin Temitope, wannan shine dalilin da yasa muke yawan fada.

"Temitope bata kaunan yaranmu domin galibi ni nake kula da su.

"Maganar gaskiya shine ta yi watsi da yaranmu uku tun a watan Oktoban 2018 ni nake kula da su," inji Oluwole.

Temitope, yar kasuwa da ke zaune a Olomi na garin Ibadan ne ta shigar da kara a kotun na neman a raba aurenta da mijinta saboda wai ba su jituwa kwata-kwata.

"Da na danyi kuskure kadan a gida sai ya rufe ni da duka, yana duka na har lokacin da na ke da juna biyu.

"Akwai lokacin da aka kwantar da ni a asibiti saboda irin dukan da ya min. Sannan yana bin mata a waje da shan giya.

"Dattawan unguwan sunyi kokarin yin sulhu tsakaninmu amma hakan bai yiwu ba. Babu sauran soyaya tsakanin mu, a raba auren kawai," Temitope ta roki kotu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel