Wata sabuwa: Faruk Lawan ne ya keta sakamakon zaben gwamnan Kano – Inji Kwamishina

Wata sabuwa: Faruk Lawan ne ya keta sakamakon zaben gwamnan Kano – Inji Kwamishina

Kwamishinan harkokin kananan hukumomi na jahar Kano, Alhaji Murtala Sulen Garo ya musanta zargin da ake masa na sa hannu cikin tayar da hankali a ofishin hukumar INEC ta karamar hukumar Nassarawa tare da mataimakin gwamna Nasiru Yusuf Gawuna da har ta kai ga sun yaga sakamakon zaben gwamna na karamar hukumar.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Murtala ya bayyana haka ne a ranar Alhamis, 14 ga watan Maris a yayin ganawa da yayi da yan jaridu a ofishinsa, inda ya ambaci sunan tsofaffin yan majalisar wakilai, Farouk Lawan da Nasiru Sule Garo a matsayin wadanda suka kekketa sakamakon zabe na mazabar Gama.

KU KARANTA: Jama’an Ganduje da na Abba gida gida sun gudanar da addu’o’in samun nasara a zaben Kano

Wata sabuwa: Faruk Lawan ne ya keta sakamakon zaben gwamnan Kano – Inji Kwamishina
Kwamishina Murtala
Asali: Facebook

Idan za’a tuna, hotunan kwamishina Murtala dana mataimakin gwamna Gawuna sun bazu a shafukan sadarwar zamani, yayin da wasu matasa suka kamashi babu ko riga a jikinsa, daga bisani Yansanda suka kwaceshi, har sai da ya kwana a hannunsu.

Sai dai a jawabinsa, Garo ya zargi jam’iyyar PDP da shirya wannan labarin kanzon kurege, inda yace magoya bayan PDP ne suka rirrikeshi da nufin hanashi shiga ofishin hukumar INEC, a dalilin haka ne suka kekketa masa riga.

Ya kara da cewa shi da Gawuna sun isa ofishin ne a lokacin da suka labarin Farouk Lawan da Nasiru sun isa ofishin yayin da tattara alkalumman sakamakon zabe da nufin tayar da hankali, har ma suka kekketa sakamakon zaben ba tare da wani yace musu uffan ba, hatta Yansanda basu yi musu komai ba.

Daga karshe Murtala yace “Bamu da cikakken yakini game da kwamishinan Yansandan jahar Kano, saboda yana goyon bayan ta’adin da PDP ke shiryawa a jahar Kano, baya mana adalci.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel