Adadin yan majalisun da jam’iyyun APC da PDP suke dasu a majalisar wakilai

Adadin yan majalisun da jam’iyyun APC da PDP suke dasu a majalisar wakilai

Yayin da hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ta kammala gudanar da zaben yan majalisun tarayya tun a makonni uku da suka gabata, majalisar ta bayyana sunayen sababbi kuma zababbun yan siyasan da suka lashe zaben shiga majalisar wakilai.

Legit.ng ta ruwaito manyan jam’iyyun Najeriya, APC da PDP ne suka fi samun yan majalisu mafi rinjaye a majalisar wakilai data kunshi yan majalisa dari uku da sittin, 360, wanda a yanzu take karkashin jagorancin kaakakin majalisa Yakubu Dogara.

KU KARANTA: Ba yau farau ba: Jerin wasu manyan zabuka 6 da basu kammalu ba tun daga shekarar 2011

Hukumar INEC ta bayyana cewa jam’iyyar APC ce kan gaba wajen adadin yan majalisa, inda ta samu yan majalisu guda dari biyu da goma sha daya, 211, yayin da jam’iyyar PDP ta samu yan majalisu guda dari da goma sha daya, 111, bambancin yan majalisa guda dari kenan a tsakaninsu.

Sauran jam’iyyun ma ba’a barsu a baya ba, inda jam’iyyar APGA ta samu yan majalisu guda shida (6), ADC ta samu uku (3), AA ta samu biyu (2), PRP ta samu biyu (2), ADP ta samu daya (1), APM ta samu daya (1) yayin da SDP ta samu daya (1), itama.

Idan aka hada adadin yan majalisun da muka lissafa zai bayar da yan majalisu dari uku da talatin da takwas, 338, yayin da sauran kujeru ashirin da biyu, 22, suke jiran hukumar zabe ta sanar dasu.

A wani labarin kuma, jam’iyyar APC ta kare ma abokiyar hamayyarta ta PDP a yawan adadin Sanatocin da suka lashe zaben shiga majalisar dattawa, majalisar data kunshi mutane 109, uku daga kowaccen jaha, sai Abuja mai Sanata guda daya, kuma take karkashin Sanata Bukola Saraki.

Bincikenmu daga sakamakon zaben Sanatoci da hukumar INEC ta sanar ya nuna jam’iyyar APC ta samu sanatoci 62, yayin da jam’iyyar PDP ta samu Sanatoci 37, YPP ta samu Sanata daya (1), yayin da sauran zabuka Tara (9) suke jiran maimaici, daga cikin zababbun Sanatocin akwai Mata guda shida.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel