Asha: An tsinci gawar matashi cikin rijiya a garin Jos

Asha: An tsinci gawar matashi cikin rijiya a garin Jos

Al'umma unguwanin Dutse Uku da Unguwan Rukuba na garin Jos na jihar Plateau na zaune cikin fargaba bayan an gano wata gawa cikin rijiya a yau Talata.

Kakakin 'yan sandan jihar, Tyopev Terna ya tabbatar da afkuwar lamarin.

Premium Times ta ruwaito cewa ya ce an aike da jami'an tsaro unguwanin domin tabbatar da doka da oda.

A cewar Mr Terna, jami'an tsaron sun kori dandazon mutane da suka fara taruwa a kusa da rijiyar domin kare barkewar rikici.

Asha: An tsinci gawar matashi cikin rijiya a garin Jos
Asha: An tsinci gawar matashi cikin rijiya a garin Jos
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: An damke wanda ake zargi da kashe dan majilisar tarayya a Oyo

"An sanar da 'yan sanda ta wayan tarho cewa an kashe wani mutum an jefa gawarsa a cikin rijiya. Rundunar 'yan sandan tayi gaggawan aikewa da jami'anta wurin da abin ya faru. Da isarsu, yan sandan sun ga gawar kuma sun duba ta.

"Yan sandan sun tarwatsa al'umma da suka taru a wurin. Yanzun an samu natsuwa a unguwanin," inji shi.

A bangarensa, Kwamishinan watsa labarai da sadarwa, Yakubu Dati ya ce kisar barazana ce ga zaman lafiya a jihar.

Mr Datti ya yabawa al'umma a kan yadda suka daure ba su tayar da fitina ba duba da abinda ya faru.

Majiyar Legit.ng ta lura cewa jami'an tsaro da suka hada da sojoji da 'yan sanda suna ta isowa unguwan.

Jihar Plateau dai tana daya daga cikin jihohin da akafi samun barkewar rikici a kasar nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel