Aikin mu shi ne kawo zaman lafiya ba kashe mutane ba – inji ‘Yan Sandan Kano

Aikin mu shi ne kawo zaman lafiya ba kashe mutane ba – inji ‘Yan Sandan Kano

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya da ke jihar Kano sun bayyana abin da ya sa ba su harbe mataimakin Gwamnan jihar Kano da kuma wani babban Kwamishina na jihar a lokacin da su ka nemi su kawo rikici a wajen zaben gwamna da aka yi.

Mataimakin gwamna, Nasiru Yusuf Gawuna da kuma Kwamishinan harkokin kananan hukumomi watau Murtala Sule Garo sun shigo inda ake tattara kuri’un zaben da aka yi a cikin karamar hukumar Nassarawa ne tare da ‘yan daba.

Wannan danyen aiki da mataimakin gwamnan da kuma Kwamishinan jihar su kayi ya jawo hatsaniya. Sai dai duk da haka jami’an tsaro ba su yi amfani da bindigogin su ba. Wani jami’in ‘Yan Sanda yace aikin su shi ne zaman lafiya.

KU KARANTA: An kama Mataimakin Gwamnan Kano yana shirin rusa zabe

Aikin mu shi ne kawo zaman lafiya ba kashe mutane ba – inji ‘Yan Sandan Kano
Alhaji Murtala Sule Garo da Alhaji Lamin Sani su na hannun hukuma
Asali: UGC

DSP Haruna Abdullahi, wanda shi ne ke magana da yawun ‘Yan Sanda na Kano ya fadawa manema labarai cewa ba aikin su bane kashe mutane, sai dai su kama wadanda ake zargi da laifi, su kuma maka su gaban hukuma ayi bincike.

Yanzu haka dai Murtala Garo da kuma shugaban hukumar Nasarawa watau Lamin Sani, sun shiga hannun ‘yan sanda da laifin keta sakamakon zabe. Jami’an tsaron za su yi bincike game da lamarin sannan kuma su sanar da jama’a.

‘Yan Sandan sun ce ba su kama Mataimakin gwamna Ganduje watau Nasiru Gawuna ba, sai dai sun dauke sa ne daga inda ake rigima domin tsare ran sa. A baya dai shugaba Buhari yayi umarni a harbe duk wanda aka kama zai saci akwati.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel