Za a sake zaben wasu mazabu a jihar Kano - INEC

Za a sake zaben wasu mazabu a jihar Kano - INEC

Bayan kammala tattara sakamakon zaben kananan hukumomi 44 na jihar Kano, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC, ta kaddamar da cewa sai an sake gudanar da zabe a mazabun wasu kananan hukumomi na jihar.

Abba da Ganduje
Abba da Ganduje
Asali: UGC

Kamar yadda shafin jaridar Daily Trust ya ruwaito, babban Bature kuma Kwamishinan zabe na jihar Kano, Farfesa Riskuwa Shehu shine ya bayyana hakan a daren yau na Litinin cikin hedikwatar INEC da ke birnin Kanon Dabo.

A cewar sa, dan takarar kujerar gwamnan jihar na jam'iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf, ya samu gamayyar kuri'u 1,014,474 yayin da dan takara na jam'iyyar APC, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya samu kuri'u 987,819.

KARANTA KUMA: Yadda sakamakon zaben gwamnan jihar Kano ya kasance

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, tun a Yammacin jiya hukumar INEC ta bayyana sakamakon kananan hukumomi 43 cikin 44 da jihar Kano ta kunsa, inda dan takara na jam'iyyar PDP ke kan gaba ta fuskar yawan adadi na gamayyar kuri'u da ya lashe.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng