Jam’iyyar APC ta yi wuju wuju da PDP a kananan hukumomi 10 na jahar Zamfara

Jam’iyyar APC ta yi wuju wuju da PDP a kananan hukumomi 10 na jahar Zamfara

Jam’iyyar APC mai mulki a jahar Zamfara ce take kan gaba a zaben gwamnan jahar daya gudana a ranar Asabar, 9 ga watan Maris, kamar yadda alkalumman sakamakon zabe da hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta sanar.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito babban baturen zabe na zaben gwamnan jahar Zamfara, Farfesa Kabiru Bala ne ya tabbatar da haka a yayin tattara sakamakon zaben gwamnan jahar da aka fara tun a ranar Lahadi, kuma ake kai har yanzu.

KU KARANTA: Akwai sake a zaben gwamnonin Adamawa, Sokoto, Bauchi da Filato – Inji INEC

Zuwa yanzu sakamakon zaben da hukumar zabe mai kanta ta sanar daga kananan hukumomi guda goma cikin kananan hukumomi goma sha hudu na jahar Zamfara sun nuna jam’iyyar APC ke kan gaba wajen yawan adadin kuri’un da ta samu, fiye da na PDP.

Baturen zabe, Farfesa Kabiru Bala ya sanar da APC ta samu kuri’u dubu dari uku da hamsin da shida da dari tara da saba’in da daya, 356, 971, yayin da jam’iyyar PDP ta keda kuri’u dubu dari da talatin da daya da dari bakwai da goma, 131,710.

Zuwa yanzu hukumar INEC ta sanar da kananan hukumomi goma da suka hada da Anka, Bakura, Birnin Magaji, Bukkuyum, Bumgudu, Gummi, Kaura Namoda, Maradun, Talata Mafara da Zurmi.

Yayin da ake dakon sakamakon zabe daga sauran kananan hukumomi guda hudu da suka hada da Tsafe, Gusau, Shinkafi, da Maru, wanda INEC tace da misalin karfe 9 na safiyar Litinin zata cigaba da aikin tattarasu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel