EthiopianAirlines: Najeriya tayi rashin Pius Adesanmi a hadarin jirgin sama
A Ranar Lahadin nan ne dai wani jirgi na kasar Habasha watau Ethiopian Airlines yayi hadari a hanyar sa ta zuwa kasar Kenya. Wannan jirgi ya tashi ne daga babban birnin Habasha na Addis Ababa.
A wannan mummunan hadarin da aka yi, mun samu labari cewa Najeriya tayi rashin Farfesa Pius Adesanmi. Wannan Malami yana cikin wadanda su ka riga mu gidan gaskiya a sanadiyyar hadarin da jirgin yayi a jiya da safe.
Farfesa Pius Adesanmi, Malami ne kuma Marubuci wanda ainihin sa ‘Dan Najeriya ne da yake zaune a kasar Canada. Manema labarai sun bayyana cewa babu shakka tuni an sanar da Iyalin Farfesan cewa ya rasu a jirgi na Boeing 737 MAX.
KU KARANTA: Dakarun Sojin Najeriya sun kashe wasu 'Yan Boko Haram
Mamacin da kuma wasu fasinjoji da ma’aikatan jirgin Ethiopian Airlines har su 157 ne su ka riga mu gidan gaskiya. Pius Adesanmi da kuma wani Bawan Allah Ambasada Abiodun Bashua kadai ne ‘Yan Najeriyan da ke cikin wannan jirgi.
Tuni dai ‘dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar adawa watau Atiku Abubakar yayi magana game da wannan rashi da aka yi. Haka kuma Jami’ar Carleton ta Canada inda Malamin yake aiki sun yi jimamin wannan babban rashi da aka yi.
Pius Adesanmi wanda aka haifa a Najeriya, malami ne a jami’a a kasar Canada, kuma ya kan yi rubuce-rubuce da-dama a gidajen jaridu. Marigayin ya kuma rubuta wani littafi da yayi fice game da Najeriya.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng