An fasa fitar da sakamakon zaben Gwamna a Kano saboda lamarin tsaro

An fasa fitar da sakamakon zaben Gwamna a Kano saboda lamarin tsaro

- Hukumar zabe ta dage sanar da sakamakon zaben 2019 na Gwamnan Jihar Kano

- INEC tace sha’anin tsaro da ake ciki a Jihar ne ya sa ta dauki wannan mataki yau

- Babban kwamishinan zabe na Kano, Riskuwa Arab-Shehu ya fadi wannan dazu

An fasa fitar da sakamakon zaben Gwamna a Kano saboda lamarin tsaro
Sai nan gaba za a ji sakamakon zaben Gwamna da Majalisa a Kano
Asali: UGC

Yanzu nan labari ya zo mana cewa Hukumar zabe na kasa mai zaman kan-ta a Najeriya watau INEC ta dakatar da bayyana zaben Gwamna a jihar Kano. INEC tace matsalar rashin zaman lafiya ya sa ta dauki wannan mataki.

Kawo yanzu an fitar da sakamakon kananan hukumomi 43 cikin 44 da ake da su a Kano. INEC tace ba za ta sanar da sakamakon na Nasarawa ba a halin yanzu. Hukumar zaben ta bayyana wannan ne ta bakin Kwamishinan ta.

KU KARANTA: An kama Mataimakin Ganduje yana neman murde zaben 2019

Farfesa Riskuwa Arab-Shehu, wanda shi ne babban jami’in zabe na Jihar Kano gaba daya, ya bayyanawa manema labarai cewa an yi yunkurin tarwatsa takardun da ke kunshe da sakamakon zaben na yankin Nasarawa a jiya da dare.

Kwamishinan na INEC yace wannan barna da aka yi masu ne ya sa za su nemo ainihin alkaluman sakamakon daga matattarar su. INEC za ta samu cikakken sakamakon zaben da aka yi a Mazabu da Gundumar Nasarawa a na’ura.

Babban kwamishinan na INEC ya kuma tabbatar da cewa za a kira dukkanin jam’iyyun da su ka shiga zaben domin ganewa idanun su a lokacin da aka fito da sakamakon zaben. Wannan ne dai zai bada damar a toshe duk kafar magudi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel