Jami’an tsaro sun cafke Gawuna da Garo ana tattara kuri’un zaben Gwamna (Bidiyo)

Jami’an tsaro sun cafke Gawuna da Garo ana tattara kuri’un zaben Gwamna (Bidiyo)

Mun samu labari cewa Rundunar 'Yan Sanda Jihar Kano sun yi ram da Maitaimakin Gwamna Nasiru Yusuf Gawuna bayan yayi kokarin sace kuri’un zaben gwamna a cikin Karamar hukumar Nasarawa.

Kamar yadda labari ya zo mana, haka shi ma Kwamishinan harkokin kananan hukumomi na Jihar Kano watau Murtala Sule Garo ya fada hannun Jami'an tsaron a lokacin da aka kama sa yana yunkurin sace kuri’un jihar.

KU KARANTA: 2019: An fafata tsakanin Jam’iyyar APC da PDP a Jihar Katsina

Jami’an tsaro sun cafke Gawuna da Garo ana tattara kuri’un zaben Gwamna (Bidiyo)
Mataimakin Gwamnan Kano Gawuna a motar 'Yan Sanda
Asali: Twitter

Manyan gwamnatin na Ganduje sun yi kokarin kawo ‘yan daba ne da nufin tada hatsaniya inda ake tattara kuri’un zaben gwamnan da aka yi a karamar hukumar Nasarawa. Yanzu dai nan ke kurum ta rage ba a bayyana ba.

Yanzu ana jiran hukumar INEC mai zaman-ta ne ta sanar da sakamakon zaben na cikin karamar hukumar Nasarawa bayan an ji cewa PDP ce ke gaba da ‘yar karamar tazara. PDP tana ikirarin ta samu gagarumar nasara a Yankin.

Mataimakin Ganduje ya shiga hannun hukuma

‘Yan Sanda sun kama Nasiru Gawuna da Murtala Garo su na neman murde zabe jiya da dare. Jami’an tsaro sun cafke na-hannun daman Ganduje ne a Nasarawa. Inda za ku ga bidiyon yadda aka yi tumu-tumu da su.

'Yan Sanda sun yi gaba da Nasiru Gawuna

Shi dai Murtala Sule Garo wanda ake yi wa lakabi da Kwamandan yakin Gwamna Ganduje a Kano, an dauke sa hoto ne yana ciki wani hali na takaici. Sule Garo, Suruki ne wajen tsohon gwamna Rabiu Kwankwaso.

Jami’an tsaro sun cafke Gawuna da Garo ana tattara kuri’un zaben Gwamna (Bidiyo)
Kwamishinan Ganduje watau Murtala Garo a tozarce
Asali: Twitter

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel