Kaduna: Shugaban PDP bai yarda da sakamakon zaben Gwamna ba

Kaduna: Shugaban PDP bai yarda da sakamakon zaben Gwamna ba

Jam’iyyar PDP ta fito ta bayyana cewa sam ba za ta amince da zaben da aka yi na gwamna da ‘yan majalisu a jihar Kaduna ba. Jam’iyyar adawar tace an tafka magudi na kin-karawa a zaben da aka yi jiya.

Shugaban jam’iyyar PDP na Kaduna, Felix Hassan Hyet, yayi ikirarin cewa wasu ne daga cikin manyan gwamnatin jihar kurum su ka zauna su ka rika kitsa sakamakon karya. Shugaban na PDP yace an yi murdiya a zaben gwamnan.

Felix Hassan Hyet yake cewa jami’an tsaro sun hana mutanen PDP yin zabe a Sanga da kuma cikin karamar hukumar Kagarko. Sannan kuma Hassan Hyet yake cewa an yi amfani da kudi wajen sayen kuri’un al’umma a irin su Zaria.

KU KARANTA: Jam'iyyar APC tana kan gaba a zaben Gwamnan Jihar Kaduna

Kaduna: Shugaban PDP bai yarda da sakamakon zaben Gwamna ba
PDP tace Isa Ashiru bai sha kashi a hannun El-Rufai ba
Asali: UGC

Jam’iyyar ta PDP ta kuma bayyana cewa an rika satar akwatunan zabe a irin su karamar hukumar Chikun inda jam’iyyar APC ba ta da karfi. Hyat yace a Birnin Gwari ma dai gaba daya babu wanda yayi zabe sai dai aka ji sakamako kurum.

Har wa yau, jam’iyya hamayyar ta koka da cewa an murde kuri’un da aka samu a yankin Rigasa da ke cikin karamar hukumar Igabi. PDP tace gwamna ne ya zabi abin da ya ga dama kurum aka kakaba a matsayin sakamakon yankin.

PDP dai tace an rika aika jami’an tsaro domun razana jama’a kuma ta tabbatar da cewa ba za ta sake ta yarda idan hukumar INEC ta sanar da abin da ya sha ban-ban da kuri’ar da mutanen ta su ka kada ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel