Jam’iyyar APC tayi nasara a rumfar akwatin Hadiza Balarabe a Sanga

Jam’iyyar APC tayi nasara a rumfar akwatin Hadiza Balarabe a Sanga

Labari ya zo mana cewa jam’iyyar APC mai mulki ce ta lashe akwatin da ke rumfar Hajiya Hadiza Balarabe, wanda ita ce Abokiyar takarar gwamna Malam Nasir El-Rufai a zaben jihar Kaduna na 2019.

‘Yar takarar mataimakin gwamnan na jihar Kaduna, Dr. Hadiza Balarabe ta samu nasarar lashe zaben da aka yi a akwatin da ta ke zabe a mazabar ta da ke cikin Unguwar Gwantu da ke karamar hukumar Sanga a jihar Kaduna.

Hadiza Balarabe ta kada kuri’ar ta ne a akwatin farko na Gwantu I da ke cikin Gundumar Gwantun da ke karamar hukumar Sanga. APC ta samu kuri’u 150 a zaben na gwamna inda jam’iyyar PDP mai hamayya ta iya samun 50.

KU KARANTA: Sakamakon zaben sabon Gwamna a Jihar Kaduna (KAI TSAYE

Jam’iyyar APC tayi nasara a rumfar akwatin Hadiza Balarabe a Sanga
El-Rufai ya doke PDP a Mazabar Abokiyar takarar sa
Asali: UGC

A zaben ‘dan majalisar dokoki na yankin, APC mai mulki dai ta tashi da kuri’a 140. ‘Dan takarar PDP wanda ya zo na biyu, ya samu kuri’u 58 ne a zaben. Mutane 200 ne su ka kada kuri’ar su a wannan akwatin da ke Gwantu.

Malam Nasir El-Rufai wanda yake neman tazarce ya dauko Musulmar mace daga Kudancin jihar Kaduna ne a matsayin mataimakiyar sa a wannan karo. An dai ta surutu na zabar Musulmar da gwamnan yayi a zaben na 2019.

Shi kuma mataimakin gwamna mai shirin barin gado watau Barnabas Bantex, ya kawowa Nasir El-Rufai akwatin sa amma ya rasa Mazabar sa hannun PDP inda ya sha kashi da fiye da kuri’a 1500.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel