Bentex ya kawo akwatin Unguwar sa, amma ya rasa Mazabar sa hannun PDP

Bentex ya kawo akwatin Unguwar sa, amma ya rasa Mazabar sa hannun PDP

Jam’iyyar adawa ta PDP ce tayi nasara a cikin Garin Manchok da ke yankin Kaura a Kudancin Kaduna. Barnabas Bala Bantex, wanda shi ne mataimakin gwamnan jihar ya fito ne daga wannan yanki.

Kamar yadda Malamin zaben na Garin Manchok ya bayyana jiya, ya tabbatar da cewa ‘dan takarar PDP watau Isa Ashiru ya doke gwamna mai-ci Malam Nasir El-Rufai na jam’iyyar APC da ratar kuri’u fiye da 1, 500 a zaben jiya.

Yusuf Taiwo, wanda shi ne jami’in da ya tattara kuri’un a jiya yace APC ta samu kuri’a 1474, yayin da PDP ta samu 2978 a zaben gwamna. A zaben ‘yan majalisar dokoki kuma APC tana da 1, 311, PDP kuma tana da 3, 036.

KU KARANTA: Jam’iyyar PDP ta lashe akwatunan gidan Gwamnatin Kaduna

Bentex ya kawo akwatin Unguwar sa, amma ya rasa Mazabar sa hannun PDP
Mazabar Mataimakin El-Rufai ta shiga hannun Isa Ashiru
Asali: Twitter

Sai dai Barnabas Bantex yayi kokarin kawo akwatin da ke rumfar ta sa da ke cikin karamar hukumar Kaura. Gwamna El-Rufai ya samu kuri’u 143 ne a akwatin zabe na 009 da ke cikin Unguwar Randiam Ninyo Allah.

‘Dan takarar PDP a zaben na gwamna watau Isa Ashiru Kudan ya kuma samu kuri’a 85 ne rak a inda mataimakin gwamnan na jihar Kaduna yake zabe. Wakilin hukumar INEC, Sufyan Ahmed ya tabbatar da wannan a jiyan.

A zaben 'Yan Majalisar Tarayya da aka yi kwanaki, inda Arch. Barnabas Bantex ya nemi Sanatan Kudancin Kaduna, ya sha kashi a hannun ‘dan takarar PDP wanda shi ne yake kan mulki a yanzu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel