Abba Yusuf ya doke APC a cikin Mazabar Ibrahim Shekarau

Abba Yusuf ya doke APC a cikin Mazabar Ibrahim Shekarau

Jam’iyyar APC mai mulki ta sha kashi a cikin Mazabar Giginyu da ke Nasarawa a zaben gwamnan da kuma ‘yan majalisun dokoki da aka yi a yau a Kano. Wannan labari ya zo mana ne ba da dadewa ba.

PDP ce tayi nasara a akwatin tsohon gwamnan jihar Kano Malam Ibrahin Shekarau da ke cikin Mazabar Giginyu a cikin karamar hukumar Nasarawa. ‘Dan takaran PDP watau Abba Yusuf ya doke Gwamna Abdullahi Ganduje.

Gwamna mai-ci Abdullahi Umar Ganduje ya samu kuri’a 91 ne yayin da PDP ta samu kuri’u 143. ‘Dan takarar PRP kuma kwamishina a lokacin Shekarau watau Malam Salihu Sagir Takai ya tashi da kuri’u 13 rak ne a zaben na yau.

KU KARANTA: Mataimakin Gwamnan Kano ya gaza kawowa APC akwatin sa

Abba Yusuf ya doke APC a cikin Mazabar Ibrahim Shekarau
Tsohon Gwamna Ibrahim Shekarau ya rasa akwatin Giginyu
Asali: Facebook

Haka kuma mu na samun labari cewa tsohon gwamna Rabiu Kwankwaso wanda yake jam’iyyar PDP a yanzu ya kawo akwatun Mazabar sa. Kwankwaso ya kada kuri’ar sa ne a Unguwar Malamai da ke cikin karamar hukumar Madobi.

Mun ji kishin-kishin din cewa Abokin takarar Abba Yusuf a PDP watau Aminu Abdussalam ya gaza kawowa jam’iyyar adawar akwatin sa. PDP ta samu kuri’a 23 ne yayin da APC ta samu kuri’a 93 a akwatin Kofar fada da ke Gwarzo.

Haka kuma ana jita-jitar cewa shi kan sa ‘dan takarar gwamnan na PDP watau Abba Kabiru Yusuf ya sha kashi a rumfar mazabar sa da ke cikin Mandawari. Ana nan ne dai Shugaban APC na Kano watau Abdullahi Abbas yake kada kuri’ar sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel