PDP ta lashe akwatin gidan Gwamnatin Jihar Kaduna a zaben Gwamna

PDP ta lashe akwatin gidan Gwamnatin Jihar Kaduna a zaben Gwamna

Yanzu nan ne labari ya zo mana cewa mai girma gwamna Malam Nasir Ahmad El-Rufai na jihar ya gaza kawo akwatin da ke cikin rumfar gidan Gwamnatin Jihar Kaduna inda yake mulki a halin yanzu.

Jam’iyyar APC mai mulki ta sha kayi ne a hannun PDP mai adawa a cikin fadar Sir Kashim Ibrahim da ke Garin Kaduna. Isa Ashiru ne PDP ya samu kuri’u 145, yayin da El-Rufai ya samu kuri’a a 114 a rumfar fadar.

Sai dai ba mu sa labari game da zaben ‘yan majalisar dokoki a akwatin na PU 013 da ke cikin fadar gwamnatin jihar Kaduna ba. A akwati na biyu (watau PU 014) da ke cikin fadar, PDP ta samu 109 yayin da APC ke da kuri’a 84.

KU KARANTA: Mataimakin Gwamnan Kano ya gaza kawowa Ganduje akwatin sa

PDP ta lashe akwatin gidan Gwamnatin Jihar Kaduna a zaben Gwamna
El-Rufai ya kawo akwatin Mazabar sa da ke Unguwar Sarki
Asali: UGC

A mazabar gwamnan kuma inda yake kada kuri’a, APC ta samu kuri’u 367. Nasir El-Rufai yayi wa babban abokin hamayyar sa watau Isa Ashiru ne PDP wanda ya samu kuri’a 59 mugun bugu ne a rumfar Unguwar Sarki.

Abdullahi Sadiq shi ne jami’in hukumar zabe mai zaman kan-ta na kasa watau INEC da ya sanar da sakamakon zaben na akwatin farko na cikin Unguwar Sarki da ke cikin karamar hukumar Kaduna ta Arewa a jihar Kaduna.

Tuni dai gwamnan ya kada kuri’ar sa ya kuma koma bakin aiki a ofishin sa duk da ana hutu. Rt. Hon. Isa Ashiru Kudan shi ne wanda yake karawa da gwamna Nasir El-Rufai’s a zaben na bana.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel