Dan takarar Accord Party ya goyi bayan APC a zaben gwamna a Oyo

Dan takarar Accord Party ya goyi bayan APC a zaben gwamna a Oyo

Jam'iyyar Accord Party (AP) a jihar Oyo ta goyi bayan dan takarar gwamna na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Adebayo Adelabu a matsayin wanda za ta zaba.

A kwanakin baya ma jam'iyyar Action Democratic Party (ADP), itama ta goyi bayan jam'iyyar na APC a jihar ta Oyo. Wannan na zuwa ne bayan gwamnan jihar, Abiola Ajimobi ya sha kaye a takarar da ya yi na kujerar sanata a jihar.

A wani sanarwa ta shugaban jam'iyyar, Cif Muda Ogunsola da sakataren jam'iyyar Dr Adebukola Ajaja suka fitar a ranar Juma'a, sun ce jam'iyar ta cimma matsayar ne a wurin taron masu ruwa da tsaki da shugabanin jam'iyyar na kananan hukumomi 33 suka hallarta.

Wani bangare na sakon ya ce: "Mun yanke shawarar goyon bayan dan takarar na APC ne saboda mun lura cewa jam'iyyar Accord ba za ta samu ikon bawa jihar Oyo shugabanci na gari da ya dace a yanzu ba.

DUBA WANNAN: Wamakko ya yi karin haske a kan zargin tarbarbarewar dangantakarsa da Sultan

Dan takarar gwamnan ACC ya marawa APC baya a jihar Oyo
Dan takarar gwamnan ACC ya marawa APC baya a jihar Oyo
Asali: Twitter

"Hakan yasa muka yi yarjejeniya da Adebayo Adelabu na jam'iyyar APC domin mu goyi bayansa a zaben da za a gudanar a ranar Asabar.

"Shugabanin Accord Party sunyi nazarin 'yan takara biyu, Seyi Makinde na PDP da Adebayo Adelabu na APC amma suka zabi dan takarar APC saboda shine ya fi basira da cancanta da zai iya kawo cigaban da ake bukata a jihar Oyo a cikin shekaru hudu masu zuwa."

Sanarwar ta ce har yanzu Accord Party jam'iyya ne mai zaman kanta sai dai tayi hadin gwiwa ne da jam'iyyar da ta dace domin cigabar jihar Oyo.

"Muna kira ga mambobin mu da magoya bayan mu a dukkan sassan jihar nan su jefawa Adelabu kuri'a a zaben ranar Asabar," inji sanarwar.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ta ruwaito cewa anyi kokarin ji ta bakin dan takarar gwamna na jam'iyyar Accord Party na jihar, Mr Saheed Ajadi domin ji ta bakinsa amma hakan bai yiwu ba saboda wayansa a kashe ta ke.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel