Yanzu-yanzu: Tsohon mataimakin gwamnan PDP a Katsina ya fita daga jam'iyyar

Yanzu-yanzu: Tsohon mataimakin gwamnan PDP a Katsina ya fita daga jam'iyyar

Tsohon mataimakin gwamna a jihar Katsina, Abdullahi Garba Faskari ya fice daga jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP inda ya ce abin kunya ne a gare shi da al'ummar Katsina idan aka bari mutumin Kano ya zama gwamna a Katsina.

A yayin da Faskari ke sanar da ficewarsa daga jam'iyyar na PDP, ya ce, "munafincin da ake tafkawa a jam'iyyar PDP ya isa haka."

Ya ce a kullum dan takarar gwamnan ya kan zo ne daga Kano domin ya gana da mutane a Katsina kuma ya koma Kano, inda ya ce "wannan ba shine irin halin da muke so daga wanda zai jagorance mu ba a Katsina"

DUBA WANNAN: Dan takarar APC da ya fadi zaben kujerar majalisar wakilai ya koma PDP

Yanzu-yanzu: Tsohon mataimakin gwamnan Katsina, Faskari ya fice daga PDP
Yanzu-yanzu: Tsohon mataimakin gwamnan Katsina, Faskari ya fice daga PDP
Asali: Twitter

"Bari Lado ya zama gwamna dai-dai ya ke da kamar Katsina tana da gwamnoni biyu, daya a Katsina daya kuma a Kano," a cewarsa.

Ya ce ba za a kwatanta cancanta tsakanoin dan takarar PDP, Senata Yakubu Lado da Aminu Masari na jam'iyyar APC ba inda ya ce, "Nayi murabus daga jam'iyyar PDP kuma a halin yanzu ba ni da jam'iyyar."

Ya ce jam'iyyar PDP ba tayi musu adalci ba tun bayan zaben cikin gida da aka gudanar inda aka saba yawancin dokokin jam'iyyar har sai da Lado ya zama dan takarar gwamna a jam'iyyar.

Faskari wanda mataimakin gwamna ne a zamanin mulkin Shehu Shema bai bayyana jam'iyyar da zai koma ba amma bisa ga dukkan alamu ana kyautata zaton jam'iyyar APC mai mulki a jihar zai shiga.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel