Tsaro: An fitar da kididdigar adadin mutanen da aka kashe a Zamfara cikin mako guda

Tsaro: An fitar da kididdigar adadin mutanen da aka kashe a Zamfara cikin mako guda

Rahotanni sun bayyana cewa a kalla mutane 113 ne aka kashe a kananan hukumomi uku na jihar Zamfara da 'yan bindiga rika kaiwa hari a cikin mako guda da ya wuce.

'Yan bindigan sun kuma lalata kadarori na miliyoyin naira.

Bayan kashe-kashen da aka rika yi a jihar, da yawa daga cikin mazauna kananan hukumomin Shinkafi, Anka da Tsafe sun bar gidajen su sun koma sansanin masu gudun hijira a jihar.

A ranar Asabar da ta gabata, rundunar 'yan sanda reshen jihar Zamfara ta ce a kalla mutane 29 ne 'yan bindiga suka kashe a karamar hukumar Shinkafi.

DUBA WANNAN: Dan takarar APC da ya fadi zaben kujerar majalisar wakilai ya koma PDP

Rashin Tsaro: A kalla mutane 113 ne aka kashe cikin mako daya a Zamfara
Rashin Tsaro: A kalla mutane 113 ne aka kashe cikin mako daya a Zamfara
Asali: Facebook

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Muhammad Shehu ya shaidawa Premium Times cewa 'yan bindigan sun tare mutanen ne yayin da suke hanyarsu ta komawa kauyen Kwari bayan sun gama cin kasuwa a garin Shinkafi.

Sai dai mazauna garin sun ce an kashe a kalla 'yan kungiyar sa kai na Civilian JTF guda 30 a kauyen Kwaren Shinkafi da ke karamar hukumar Shinkafi.

An kai wannan harin ne kwanaki biyu bayan harin da aka kai garin Shinkafi.

Mazaunin garin, Bala Shinkafi ya shaidawa Blue Print cewa 'yan bindigan da adadinsu ya kai 100 sun yiwa 'yan Civilian JTF din kwantar bauna ne a yayin da suke yiwa 'yan kasuwan rakiya daga garin Kware zuwa Shinkafi a ranar kasuwan.

Ya ce 'yan kasuwa da yawa sun jikkata sannan 'yan bindigan sun sace musu kayayakinsu.

"Mun birne a kalla mutane 31 yayin da wadanda suka jikkata an garzaya da su zuwa babban asibitin Shinkafi domin basu kulawa ta musamman," inji Bala Shinkafi.

'Yan bindigan sun sake kai sabuwar hari a ranar Lahadi inda suka kashe 'yan Civilian JTF 20 a garin Danjibga a karamar hukumar Tsafe.

Wani mazaunin garin, Mustapha Danjibga ya shaidawa Blueprint cewa 'yan bindigan sun shigo garin ne a kan babura misalin karfe 1 na rana.

Sai dai 'yan Civilian JTF din sun fattatake su.

"A yayin musayar wutan da 'yan bindigan a garuruwan Kwaren Ganuwa da Keta, mun rasa mambobin mu guda 23," inji Mr Danjigba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel