Fasto Iginla ya bayyana yadda ya rika neman mata yayin da yake da aure

Fasto Iginla ya bayyana yadda ya rika neman mata yayin da yake da aure

Babban faston nan da ke Abuja mai suna Joshua Iginla, na cocin Champions Royal Assembly da ke cikin Garin Kubwa a birnin tarayya, ya fito da bakin sa yana bayyana irin fasikancin da yayi da 'yan mata a da.

Fasto Joshua Iginla ya bayyanawa Duniya cewa ya taba cin amanar Mai dakin sa da wata yarinya a lokacin yana gidan aure. Malamin na addinin kirista ya bada wannan labari ne a kan mimbari a Ranar Lahadin da ta gabata.

A hudubar wannan fasto, yace sun samu matsala a da can, da shi da maid akin sa a dalilin kwanciya da yake yi da wasu ‘yan mata daban. Shehin yake cewa wannan ya saura kiris igiyar auren sa ta kwance a sakamakon hakan.

Wannan malami ya kuma bada labarin yadda Mai dakin sa ta je ta hadu da wani mutumi daban kuma har su ka samu yaro a dalilin hakan a cikin gidan sa. Shi ma kuwa dai yace wata matar aure ta taba haifa masa yaron shege.

KU KARANTA: Abubuwan da ba ka sani ba a kan Obasanjo wanda ya cika shekaru 82

Fasto Iginla ya bayyana yadda ya rika neman mata yayin da yake da aure
Malamin Kirista Iginla ya tonawa kan sa asiri da kan sa a gaban jama'a
Asali: UGC

Malamin addinin yace a lokacin da ya gano irin barnar da Uwargidar sa take yi, sai ya rufa mata asiri, amma Malamin yace matar sa ta taso sa gaba bayan an same shi da irin wannan laifi, har ta kai ana nuna sa ana masa dariya.

John Iginla yayi kira ga Mabiyan sa da su rika yi wa shugabannin su addu’a a ko yaushe. Faston ya bada labarai iri-iri na yadda yayi tunanin rabuwa da matar sa amma yayi hakuri saboda a rufawa juna asiri a matsayin sa na Malami

Wannan babban Limami yayi kaurin suna wajen rabawa Mabiyan sa manyan kyaututtuka har da motoci na zamani idan yana wa’azi. Ba a sani ba ko Mai dakin ta sa ta na cikin cocin wannan karo dai da yayi wa kan sa tonon silili.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel