Sunayen yan siyasa 18 dake muradin darewa kujerar gwamnan jahar Borno
Akalla jam’iyyu arba’in da daya ne suka tsayar da yan takara daban daban da zasu wakilcesu a fafatawar da za’ayi a zaben gwamnan jahar Borno a ranar Asabar, 9 ga watan Maris, kamar yadda kwamishinan hukumar INEC, reshen jahar Borno ya bayyana.
Legit.ng ta ruwaito kwmaishinan mai suna Mohammed Ibrahim ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da manema labaru a ranar Laraba, 6 ga watan Maris, inda yace daga cikin jam’yyu 41 da suka tsayar da yan takara har da APC da PDP.
KU KARANTA: An bude asusun neman taimako dan taimaka ma Atiku ya kai karar Buhari gaban kotu
Bugu da kari, Ibrahim yace akwai yan takarkarun kujerun majalisar dokokin jahar Borno da adadinsu ya kai dari hudu da saba’in da takwas, 478, kamar yadda jam’iyyun suka mika musu.
Daga karshe Ibrahim ya bada tabbacin shirin hukumar zabe mai zaman kanta, INEC na gudanar da ingantaccen zabe a jahar Borno, inda yace daga ranar Alhamis zasu fara aika kayan zaben zuwa kananan hukumomi.
Ga jerin wasu yan takarar gwamnan jahar Borno su goma sha takwas;
APC – Farfesa Babagana Zulum
IDP - Rufai Munguno
SDP - ABBA MODU
PDP – Muhammad Imam
ANRP- - Ahmed Dikwa
ZLP – Ibrahim Mshelia
AD – Mukhtar Abdullahi
ADC – Muhammad Khalajinda
APP - UMAR ALI DIMARI
DPP - YUSUF KACHALLAH
GPN - MOHAMMED SHEHU LAMINU
NPM - ADAMU ALI
NRM - MUSTAPHA UMAR MUSTAFA
PPA - BABAGANA MUSA K
PPN - UMAR MUSTAPHA
UPN - USMAN BABA
UP - ALH. BAKO ALI BARMA
YES - BABAGANA MOHAMMED
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng