Uwa-mabada-mama: Najeriya ta samu babban matsayi a majalisar dinkin duniya

Uwa-mabada-mama: Najeriya ta samu babban matsayi a majalisar dinkin duniya

Kasar Najeriya dai kamar yadda muka samu yanzu haka ta samu wani babban matsayi a majalisar dinkin duniya inda ta karbi ragamar shugabancin kungiyar 'yan Afrika a majalisar ta dinkin duniya a watan Maris.

Babban jakada kuma Sakataren din din din a majalisar dinkin duniya dake wakiltar Najeriya Farfesa Tijjani Bande shi ne ya karbi ragamar shugabancin kungiyar daga hannun kasar jamhuriyar Benin a wurin wani kayataccen bikin da akayi a garin New York.

Uwa-mabada-mama: Najeriya ta samu babban matsayi a majalisar dinkin duniya
Uwa-mabada-mama: Najeriya ta samu babban matsayi a majalisar dinkin duniya
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kwararren Lauya ya karfafawa Atiku gwuiwar neman hakkin sa a kotu

Legit.ng Hausa ta samu cewa da yake jawabin godiya bayan karbar jagorancin kungiyar, Farfesa Bande ya sha alwashin yin shugabanci na gari da za'ayi koyi da shi a duniya baki daya.

Yace kuma zai yi anfani da matsayin sa wajen ganin ya hada kan 'yan kasar baki daya tare kuma da tabbatar da zaman lafiyar nahiyar da dorewar kyakkyawan shugabanci.

A wani labarin kuma, Hukumar nan ta gwamnatin tarayya dake yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) ta sanar da samun nasarar cafke wani mai suna Azeez Afolayan da ya ke damfarar mutane da sunan Hamid Ali.

Kamar yadda muka samu dai, shi Azeez Afolayan wanda yanzu haka yake garkame a dakunan ajiyar masu laifi na hukumar ta Economic and Financial Crimes Commission (EFCC), ya shahara ne wajen karbar kudaden mutane da sunan zai samar masu aiki a hukumar Kwastam.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel