Al'ajabi: 'Yan Najeriya 5 da ke ikirarin sun mutu, sun shiga aljannan sun dawo

Al'ajabi: 'Yan Najeriya 5 da ke ikirarin sun mutu, sun shiga aljannan sun dawo

A Najeriya dai addini abu ne mai muhimmanci inda akwai addinai da dama a kasar tare da dariku da dama. Addinin kirista yana daga cikin addinin da ke da mabiya masu yawa a Najeriya kuma a cikinsa akwai dariku daban-daban masu aikata abubuwan ban mamaki.

Daya daga cikin abubuwan ban mamakin shine batun dawo da rai ga mutanen da suka mutu. Kuma baya ga haka wadanda suka mutun sukan yi ikirarin cewa sun ziyarci aljanna ko wuta.

Wasu daga cikinsu ma ne cewa Allah ya karbi rayuwarsu domin ya nuna musu na'imomin da ke aljanna ko azabar da ke wuta.

Bayan an dawo musu da ransu, galibinsu na ikirarin cewa ba su so dawowa ba amma an dawo da su ne domin su isar da muhimman sako a kan abubuwan da suka gani.

Gai dai biyar daga cikin mutanen da suka shahara a kan cewa sun tafi lahira sun ziyarci wuta ko aljanna sannan suka dawo.

DUBA WANNAN: Zaben 2019: Mu ne mu kayi nasara - Buba Galadima

1. Abraham Yakubu

Abraham Yakubu da musulmi ne amma daga bisani ya koma addinin Kirista bayan wai ya yi hatsari kuma ya mutu. An ce wai likitoci sun tabbatar da cewa ya mutu.

Sai dai a yayin gawarsa ke kwance, Abraham Yakubu ya ce an tafi da shi wuta da aljanna inda aka nuna masa wasu abubuwa kuma daga bisani aka dawo masa da ransa domin ya fadakar da al'umma.

A 2016, Abraham Yakubu ya shahara a tsakanin Kiristoci. Duk da cewa kafin shi wasu mutane sunyi ikirarin sun mutu sun dawo amma kasancewar shi musulmi ne da farko kafin ya zama kirista ya sanya mutane da dama razana idan sun ji labarinsa. Bayan wani dan lokaci, labarinsa ya lafa.

Al'ajabi: 'Yan Najeriya 5 da ke ikirarin sun mutu, sun shiga aljannan sun dawo
Al'ajabi: 'Yan Najeriya 5 da ke ikirarin sun mutu, sun shiga aljannan sun dawo
Asali: Twitter

2. Shotunde Kayode

A 'yan kwanakin nan, wani fasto a 'Uncommon Favour Evangelical Ministry da ke Ibadan a jihar Oyo ya bayyan yadda ya tafi aljanna kuma ya dawo. Mutumin mai suna Shotunde Kayode ya ce bai san komi game da addini ba amma ya yi hatsarin mota da wasu mutane 17.

An ajiye gawarsa a asibiti tsawon kwanaki 3 domin ba a san iyalansa ba. A cikin kwanaki ukun ne ya ce an tafi da shi aljannan. Ya ce daga nan ne Ubangiji ya ce ya kafa coci idan ya dawo domin ya fadakar da al'umma abinda ya gani.

3. Bishop Susan Ziki Dube

Bishop Susan itace wadda ta kafa Holy Baptist Apostolic Church of Africa. A cewarta, ta dade tana yiwa mutane addu'a tun tana shekara 19 amma abinda ya sanya ta kafa coci shine ta bata mutuwa a asibiti.

Yayin da malaman lafiya ke jira likita ya zo su fada masa cewa ta mutu, ta ga kanta a aljanna. Ta wuce sama na daya, biyu da na uku anan ne ta ga mala'ika wanda ya fada mata ta tafi ta kafa coci kuma hakan ya faru.

4. Samuel Tega

Samuel yaro ne dan asalin jihar Edo mai shekaru 10 da ya yi ikirarin shima ya tafi aljanna ya dawo. Shima Samuel Tega ya zama mai wa'azi yanzu inda ya ke fadawa al'umma abubuwan da ya gano a can.

5. Margaret Amure

Margaret itama wata mace ne da tayi ikirarin ta tafi aljanna ta dawo. Ta fitar da bidiyo a lokaci guda da Samuel inda ta ke bayanin abinda ta gano a aljanna da aka rika sayarwa a Najeriya. Sai dai labarinsu bai yi suna sosai ba saboda wata Linda Ngaujah 'yar kasar Sierra Leon ta razana Afirka ta irin bayannai masu tsawo har ma da lissafa sunayen fastoci da wasu manyan mutane da ta gani a aljanna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarkre da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel