Abubuwa 7 da zasu tabbatar da wanda zai lashe takarar gwamnan jahar Kaduna

Abubuwa 7 da zasu tabbatar da wanda zai lashe takarar gwamnan jahar Kaduna

A yau saura kwanaki uku a gudanar da zabukan gwamnoni a sama da jahohin Najeriya talatin, 30, inda a jahar Kaduna ake sa ran fafatawa tsakanin yan takarar manyan jam’iyyun siyasan Najeriya, watau jam’iyyar APC da jam’iyyar PDP.

Jam’iyyar APC da ludayinta ke kan dawo ta tsayar da Gwamna Nasir Ahmad El-Rufai domin ya zarce tare da cigaba da yin dare dare akan madadan iko, yayin da PDP ta tsayar da tsohon dan majalisa, Alhaji Isa Ashiru don ya kwace mulki daga hannun Malam.

KU KARANTA: An bankado shirin wasu yan siyasa na danganta Ganduje da wani mummunan abin kunya

Abubuwa 7 da zasu tabbatar da wanda zai lashe takarar gwamnan jahar Kaduna
El-Rufai da Ashiru
Asali: UGC

Sai dai binciken jaridar Premium Times ya bankado wasu muhimman ababe da sune zasu yi ruwa suyi tsaki wajen tabbatar da wanda yar nune ta nuna zai lashe zaben na ranar Asabar, 9 ga watan Maris tsakanin jiga jigan biyu.

Bambamcin kudanci da Arewacin Kaduna

Akwai bambamce bambamce na siyasa, addini, da kabilanci tsakanin yankin kudanci da Arewacin jahar Kaduna, yayin da mafi yawan kiristoci yan asalin Kaduna suka taru a kudanci, Musulmai kuma sun yi bake bake a Arewaci.

Haka zalika Hausawa Musulmai ne suka fi yawa a Arewacin, yayin da sauran kabilun jahar suka mamaye kudancin jahar, sai dai Arewacin jahar ta fi yawan jama’a da yawan kananan hukumomi, kuma nan ne inda El-Rufai yafi karfi.

Ikon da mulki

Kasantuwar El-Rufai ne ke jan ragamar mulkin jahar Kaduna, hakan yasa a lungu da sako ana jin duriyarsa, walau fastansa, wakokinsa, ko kuma irin manyan ayyukan daya shimfida a jahar, yayin da PDP kuwa sai dai tayi alkawarin ayyukan da za ta yi, don haka anan ma El-Rufai zai iya samun tagomashi.

Tafiyar hadaka

Tun bayan rikicin cikin gida data kunno kai a farfajiyar jam’iyyar ta jahar Kaduna, wanda hakan ta sabbaba fitattun yayanta suka fice suka kuma koma gefe guda inda suka hada karfi da karfe da jam’iyyar PDP, hakan ka iya ma kawo ma El-Rufai tasgaro, ya kuma baiwa Ashiru tagomashi.

Daga cikin ire iren fusatattun yan siyasan da suka fice akwai Hakim Baba Ahmed, Suleiman Hunkuyi, Isa Ashiru, Yaro Makama, Tijjani Ramalan, inda suka hada kai da tsohon gwamna Ahmed Makarfi, Danjuma La’ah, Ramalan Yero da sauransu.

Mataimakin gwamna

A wani sabon salo da ba’a saba gani a siyasar Kaduna ba, El-Rufai ya dauko mace Musulma daga kundancin Kaduna, Hadiza Balarabe don ta zamo masa mataimakiyar gwamna, yayin da Isa Ashiru na PDP ya dauko namiji kirista daga kudanci.

Hakan yasa yan kiristocin kudancin Kaduna suke ganin El-Rufai ya nuna musu ba’a tare, don haka suka zasu nuna masa ba’a tare, duk kuwa da Hadiza yar kudancin Kaduna ce.

Tsauraran matakai

Duk wanda ya san El-Rufai ya san mutum ne da baya shayin daukan tsauraran matakai idan aka zo batun gudanar da aiki, inda a jahar Kaduna ma ya sallami akalla Malamai 22,000 saboda rashin inganci, ya maye gurbinsu da sabbin malamai 25,000. Haka zalika ya sallami hakimai da dakatai 4776.

Ire iren tsauraran matakan nan sun jama’a da dama sun dauki alwashin tikashi da kasa idan aka zo zaben gwamna a jahar Kaduna, da wannan a iya cewa Isa Ashiru ne zai samu kuri’unsu.

Kashe kashe a Kaduna

Tashin hankalin da ake yawan samu sakamakon hare hare da kashe kashe da kuma barnata dukiya a yankin kudancin Kaduna, da kuma yankin Birnin Gwari yasa jama’a na ganin tamkar gwamnatin ta gaza, don haka suke tunanin zaben wanda zai kawo karshen matsalar tsaro a jahar.

Kuri’un yan shia

Duk da cewa ana ganin kamar mabiya addinin shi’anci basa zabe, amma rahotanni sun bayyana cewa a wannan karo zasu yi, kuma a shirye suke su kayar da El-Rufai sakamakon cigaba da tsare jagoranci Ibrahim Zakzaky da gwamnati ke yi, da kuma maka shi kotu da gwamnatin El-Rufai tayi.

Sai dai sakamakon zaben shugaban kasa a jahar Kaduna bai nuna hakan ba, saboda ko a Zariya, inda ake ganin sun fi yawa, PDP bata tabuka komai a zaben ba, yayin da Buhari ya samu kuri’u 111,082, amma Atiku ya tashi 23,882.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel