Murnar samun nasarar Buhari: Matashi ya fara tattaki daga Legas zuwa Abuja

Murnar samun nasarar Buhari: Matashi ya fara tattaki daga Legas zuwa Abuja

Wani matashi dan asalin jahar Kano mai suna Bashir Dalhatu Rano ya fara wani tattaki daga garin Legas inda yayi nufin isa babban birnin tarayya Abuja a kasa domin bayyana farin cikinsa da nasarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu a zabe 2019.

Majiyar Legit.ng data tattauna da Malam Bashir ta ruwaito wannan tattaki ya samo asali ne sakamakon wani musu daya kaure tsakaninsa da wasu abokanansa da suke ganin Buhari ba zai kai bantensa a zaben 2019 ba, inda shi kuma yayi alkawarin yin wannan tattaki idan har Buhari ya samu nasara akan Atiku.

KU KARANTA: Da dumi dumi: Babbar kotu ta kori surukin Kwankwaso daga takarar gwamnan jahar Kano

Haka kuwa aka yi, inda bayan sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben shugabancin kasar, sai Malam Bashir ya shiga shirin cika wannan alwashi daya dauka na takawa daga Legas zuwa Abuja a kasa.

A yanzu haka majiyarmu ta ruwaito Malam Bashir ya kai ogere, hanyar zuwa garin Ibadan na jahar Legas, inda daga nan zai dumfari babban birnin tarayya Abuja, kuma yace jama’a da dama sun bashi rubutattun sako don ya mika ma shugaba Buhari idan har ya samu ganinsa.

“Na fara tattakin ne daga idoro badiya cikin garin Legas, bayan musun da muka yi da abokaina akan nasarar Buhari, bana shakkar faruwar wani abu akan hanya saboda na san duk abinda ya sameni haka Allah ya nufa.

“Kaya guda biyu na dauka kawai, sai ruwa, sai kuma addu’o’I da jama’a ke mini, kuma wadannan addu’o’I sun bani kwarin gwiwa.” Inji Malam Bashir Dalhatu Rano.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel