Shugabannin jam’iyyar PDP a jihar Yobe sun canja sheka zuwa APC

Shugabannin jam’iyyar PDP a jihar Yobe sun canja sheka zuwa APC

Kasa da shekaru 10 bayan shugaban jam’iyyar PD a jihar Yobe ya canja sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki, Karin wasu shugabannin jam’iyyar sun bi sahun tsohon shugaban na su.

A yau, Lahadi, ne Ali Makinta, tsohon shugaban jam’iyyar PDP, da wasu shugabannin mazabu 9 su ka canja sheka zuwa APC a karamar hukumar Machina.

Da ya ke jawabi yayin karbar wadanda su ka canja shekar, Mai Mala Buni, dan takarar gwaman jihar Yobe a karkashin inuwar jam’iyyar APC, ya bukaci jama’a su fito kwai da kwarkwata domin kada wa APC kuri’a a zaben ranar Asabar, 9 ga watan Maris.

Buni ya ce fitowar jama’a a zaben gwamna da na ‘yan majalisar dokoki zai tabbatar wa da jama’a cewar babu magudi a kuri’un da shugaba Buhari ya samu a jihar.

Jam’iyyar PDP na zargin cewar an kirkiri adadin kuri’un da shugaba Buhari ya samu a jihar Yobe.

“Ya kamata mu yi amfani da zaben ranar Asabar mao zuwa domin kare kuri’un da shugaban kasa a jihar mu, a cewar Buni.

Shugabannin jam’iyyar PDP a jihar Yobe sun canja sheka zuwa APC
Shugabann jam’iyyar PDP na jihar Yobe da ya canja sheka zuwa APC
Asali: Twitter

Da ya ke Magana amadadin wadanda su ka canja shekar, Makinta ya bayyana jam’iyyar PDP a matsayin gawa da babu abinda za ta amfani kasa da shi.

Za mu yi tururuwar fitowa a zaben gwamnoni domin kada kuri’un mu ga jam’iyyar APC kamar yadda mu ka yi a zaben shugaban kasa,” a cewar Makinta.

DUBA WANNAN: Harin ‘yan daba: Gwamna Dankwambo ya tsallake rijiya da baya

A nasa bangaren, Sanata Ahmad Lawan, ja goran jam’iyyar APC a Yobe ya jinjina wa jama’ar jihar bisa irin tarbiyyar siyasa da su ke da ita.

Tun shekarar 1999 jihar Yobe ke biyayya ga jam’iyyar adawa har zuwa shekarar 2015 lokacin da jam’iyun adawa su ka dunkule su ka kirkiri APC.

“Zaben gwamna da na ‘yan majalisar dokoki zai kasance tamkar maimaici ne na abinda ya saba faruwa a baya,” a kalama Lawan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel