Radadin kaye: Masoyin Atiku ya hana wani mabaraci sadaka (Bidiyo)

Radadin kaye: Masoyin Atiku ya hana wani mabaraci sadaka (Bidiyo)

- Wani masoyin tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya bayyana rashin jin dadinsa a kan kayen da dan takarar shugaban kasa na PDP ya sha a zaben 2019

- Masoyin Atikun mai suna Olayinka Samuel ya yanke shawarar dena bawa mabarata sadaka bayan Atiku ya sha kaye a zabe

- Samuel ya yi imanin cewa mabaratan suna daga cikin wadanda suka jefawa Buhari kuri'a a zaben da aka gudanar a ranar Asabar da ya yi nasara

Wani masoyin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP Atiku Abubakar mai suna Olayinka Samuel ya hana mabarata sadaka saboda ya yi imanin suna daga cikin wadanda suka kada wa Shugaba Muhammadu Buhari kuri'a a zaben ranar 23 ga watan Fabrairu.

Legit.ng ta ruwaito cewa Shugaba Buhari na jam'iyyar APC ya samu kuri'u 15,191,847 inda ya doke abokin hammayarsa Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP da ya samu 11,262,978.

Samuel ya wallafa bidiyo a shafinsa na Twitter a ranar Juma'a 1 ga watan Maris inda ya ke cikin motarsa yana fadawa wani mai bara cewa ba zai bashi kudinsa ba.

DUBA WANNAN: Zaben Shugaban kasa: Dattawan Arewa sunyi tsokaci a kan nasarar Buhari

Ga abinda ya rubuta a shafinsa na Twitter:

"Ka dena tambaya ta kudi !!!!

Ai mun shiga Next Level yanzu .....

Dukkan mu za mu dandana abinda ta kunsa

Mu cigaba da morewa tare har har mulkin ta kare."

Wasu na ganin bai dace a nunawa mutane banbanci saboda ra'ayinsu na siyasa ba saboda zabe yana zuwa kuma ya tafi.

A baya Legit.ng ta ruwaito muku mabanbantan ra'ayoyin 'yan Najeriya game da zaben da Buhari ya lashe na ranar 23 ga watan Fabarairu.

Yayin da wasu ke muranar yadda sakamakon zaben ta kasance, wasu kuma ba su ji dadi ba a kan nasarar ta Buhari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel